Home Back

Barnar Da Isra’ila Ke Ci Gaba Da Yi A Gaza

leadership.ng 2024/5/15
Gaza

Tashin hankali da cin zarafin da Yahudawa ke yi a kan yankin Gaza da ke Gabas ta tsakiya ya fara tada zuciyar duk wani dan adam ba tare da bambancin yankin da ya fito ba ko addininsa ko kuma irin akidar siyasar da yake yi. Duk da irin munin abin da muke gani na tashin hankali a kasar Yukrain kadan wannan kadan ne a kan abin da yake faruwa na rashin imani a kan al’ummar Falasdinawa na yankin Gaza, na nuna karfin da Isra’ila ke yi a kan al’ummar Falasdin da sunan yaki da kungiyar Hamas.

Wannan yakin na baya-bayan nan ya fara ne a ranar 7 ga watan Oktoba 2023, bayan da kungiyar Hamas ta kai wani wawan hari a cikin kasar Isra’ila inda suka samu nasarar kashe wasu mutane da dama suka kuma yi garkuwa da wasu . Wannan harin ya matukar kunyata Isra’ila wadda take da tunanin ba zai yiwu a kai masu irin wanna harin ba saboda karfin jami’an tsaronta da kuma yadda ta yi suna a duniya na cewa ita kasa ce mai karfin sojoji da kuma rundunar leken asiri mafi inganci a duniya amma dakarun Hamas suka shiga har cikin Isra’ila suka yi masu ta’asar da ta kunyata su sosai a idon duniya.

Ra’ayin wannan jaridar shi ne, halin da Gaza ke ciki a wannna lokacin ba lokaci ne na neman wanda yake da laifi ba, duk da cewa, wasu na ganin ai kungiyar Hamas ce ta fara kai hari a kan Is’ra’ila a wannan karon, a harin da suka kai a ranar 7 ga watan Oktoba na shekarar 2023, amma kuma wannan cin zalin ya yi yawa. A kan haka ne ma Sakataren tsaron Amurka,Lloyd James Austin, ya bayyana cewa, ko Isra’ila ta shafe Hamas daga doron kasa ne ba wata gwaninta ta yi ba, ita ce dai ta yi asara.

Abin da ke faruwa a Gaza a halin yanzu abu ne da ya zama kalubale ga duk wani da ke da halin bayar da gudunmawar ganin an dakatar da yakin ya kuma kasa, saboda haka ya kamata dukkan wani mai yi wa duniya fatan alhairi ya kawo tasa gudummawar don ganin an dakatar da cin zalin da Yahudawa ke yi wa al’ummar Faladinawa na kashe kananan yara da mata a kullun garin Allah ya waye.

Duk da cewa, ana iya yin Allah wadai da abin da dakarun Hamas suka yi na kai hari a ranar 7 ga watan Oktoba 2023 amma kuma martanin da Yahudawa ke mayarwa a kan zirin Gaza zuwa yanzu babu hankali a cikin shi, abu ne da Shugaban Kasar Amurka Joe Biden, ya nuna a matsayin rashin hankali ya kuma nuna rashin jin dadinsa a kan yadda Isra’ila ke ta kashe al’umma babu kakkautawa.

Ba za mu bari siyasar da ke tattare da lamarin rikicin Falasdinawa ta dauke mana hankali ba.Gaza, wani yanki ne da ke da al’umma Falasdinawa masu tarin yawa suna kuma ganin dole Yahudawa ‘yan kama wuri zauna su bar masu yankinsu, amma kuma abin lura a nan shi ne, Yahudawa da Faladinawa dukkan su daga tsatso daya ne na Annabi Ibrahim a kan haka ne ya kamata su fahimci cewa, dole su yi hakuri da juna su zauna da juna lafiya a matsayin kasa biyu masu ‘yanci, kowa ya mutunta abokan zamansa.

A wannan halin ana iya cewa, fada ne a tsakanin ‘yan uwa, amma kuma a halin yanzu fadan yana neman daukar wani sabon salo da ya zama dole duniya ta tsayu don ganin an kawo karshen rasa rayukan da ake yi.

A ra’ayinmu, abin da yake faruwa a Gaza yana fito da munafuncin kasashen Larabawa ne, daga dukkan alamu kasashen Larabawa basu son ganin an kawo karshen wannan yakin. Sun gwammace su rika hankoron kai agajin abinci da sauran su, wannan lamarin bayar da gudummawa ganin an kawo karshen yakin Babban dalilin su na kin tsayuwar ganin an kawo karshen yakin, wani abu ne da kowa ya sani.

Haka kuma rikicin na Gaza ya kara bayyana munafuncin kasar Amurka wadda ta yi watsi da ra’ayoyin kasashen duniya ta ci gaba da ba Yahudawa goyon baya a yakin da take yi da al’ummar Falasdinawa.

Ba kowa ne yake maraba da matsayar Amurka a wannan rikicin ba musamman ganin yadda take dakile duk wani kokarin da kasashen duniya suke yi na ganin an kawo karshen cin zalin da Yahudawa suke yi wa mata da kananan yara a zirin Gaza,kowa ya san yadda Amurka ke ba Yahudawa makaman yaki da kuma yadda take kawar da kai ga laifukkan yaki da Yahudawa ke aikatawa a zirin Gaza.

A ra’ayinmu yakin da ake yi a Gaza da kuma wanda ake yi a Yukrain sun kara bayyana cikakken munafincin kasar Amurka, hakanan kuma munafincin Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana, a halin yanzu sun zama ‘yan amshin shata, basu da wani tasiri a idon duniya domin da kansu suke dakile duk wani kokarin da ake yi na kawo karshen cin zarafin al’umma.

Duk da wannan halin da ake ciki muna kira ga al’ummar duniya maza da mata daga dukkan bangarori ba tare da bambancin siyasa ko na addini ba, su hada hannu su tabbatar da an kawo karshen cin zarafin bil adam a Gaza. Tabbas wannan yakin ba zai amfani kowa daga bangarorin Falasdinawa da Yahudawa ba gaba daya.

People are also reading