Home Back

NAF Ta Hallaka ‘Yan Bindiga 29 A Katsina

leadership.ng 2024/7/6
NAF Ta Hallaka ‘Yan Bindiga 29 A Katsina

Rundunar sojin saman Nijeriya ta yi nasarar kashe ‘yan bindiga 29 a wani samame da ta kai a karamar hukumar Bakori a Jihar Katsina.

Nasarar na zuwa ne bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a baya-bayan nan a karamar hukumar Kankara a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuni, 2024.

Babban sakataren yada labaran gwamna Umaru Radda na Jihar Katsina, Ibrahim Kaula, ya bayyana cewa harin da aka kai ta sama a kusa da tsaunin Bakori da Yartsintsiya, a karamar hukumar Kankara ya yi sanadiyar mutuwar wasu ‘yan bindiga 29.

Ya ce, “A cewar rahotanni, harin da aka kai ta sama ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindiga takwas, inda 21 daga cikinsu suka samu raunuka.

“Daga cikin wadanda aka kubutar har da ‘yar Hakimin kauyen Ruwan Godiya, wadda aka yi garkuwa da ita tsawon watanni,” in ji Kaula.

Ya kara da cewa NAF za ta ci gaba da hadin gwiwa da sojojin kasa da hukumomin leken asiri don gano tare da kawar da masu aikata laifuka a yankin.

People are also reading