Home Back

Kano: Jigon APC Ya Fadi Hanya Mafi Sauƙi da Kwankwaso Zai Samu Shugabancin Najeriya

legit.ng 2024/5/17
  • Tsohon mataimakin shugaban APC a Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya yi magana kan takarar Sanata Rabiu Kwankwaso
  • Salihu ya ce zai yi wahala Kwankwaso ya samu abin da ya ke nema har sai idan APC ta bashi dama domin gyara matsalolinsa
  • Jigon APC ya bayyana haka ne yayin hira da 'yan jaridu inda ya ce matsalar Ganduje da Kwankwaso siyasa ce kawai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jigon jami'yyar APC, Salihu Lukman ya yi magana kan takarar shugabancin Sanata Rabiu Kwankwaso.

Lukman ya ce zai yi wahala Kwankwaso ya yi tasiri a jam'iyyar NNPP kan muradinsa na neman shugabancin Najeriya.

Jigon APC ya bayyana haka ne a yau Laraba 24 ga watan Afrilu yayin hira da gidan talabijin na Channels TV.

Ya ce jam'iyyar APC za ta iya taimaka masa wurin bude masa kofa domin ya shigo tare da gyara matsalolinsa a ƙasar.

Har ila yau, Lukman ya ce za a iya dakile matsalar Ganduje da Kwankwaso tun farko wanda jam'iyyar ta yi sakaci har Sanatan ya watsar da APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya kamata mu tura Ganduje domin sake gyara komaɗar da aka samu tun da siyasa ce ta jawo, ta haka ne kawai za a gyara matsalar."

- Salihu Lukman

Bayanai na biyo baya...

Asali: Legit.ng

People are also reading