Home Back

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da aikin titinan Naira biliyan 11 a yankunan karkara 10

premiumtimesng.com 2024/7/1
Ƴan Adawa su jira su ga irin abinda zan yi wa Kanawa a cikin wa’adin mulki na tukunna – Gwamna Yusuf

Gwamna Abba Kabir-Yusif Yusuf na Jihar Kano ya ƙaddamar da fara aikin gina titina masu jimillar tsawon kilomita 70 a yankunan karkarar mazaɓun sanatocin jihar guda uku.

Aikin wanda zai ci sama da Naira biliyan 11, an ƙaddamar da shi ne tare da haɗin guiwar IsDB, LLF.

Gwamnan da kan sa ya ƙaddamar da aikin a ranar Alhamis, a Rijiyar Gwangwan da Mil Goma, cikin Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu.

Cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna, Sanusi Bature ya fitar a ranar Alhamis ya manema labarai, ya ce wuraren biyu za su Rijiyar Gwangwan da Mil Goma za su samu titina masu tsawon kilomita 14.7 kowanen su, daga cikin titina masu jimillar tsawon kilomita 70 da za a gina.

Za a gina titinan ƙarƙashin haɗin gwiwa da Babban Bankin Musulunci da kuma Gidauniyar ‘Lives & Livelihood Fund, a ƙarƙashin shirin Raya Yankunan Karkara (KSASP), da ke ƙarƙashin (KNARDA).

Yayin ƙaddamar da aikin, Gwamna Abba ya ce gwamnatin sa ta ƙudiri aniyar yin ayyukan raya jihar da inganta rayuwar al’ummar Jihar Kano da yankunan karkara baki ɗaya.

Sanarwar ta ce aikin zai ci sama da Naira biliyan 11.

“A Dawakin Kudu, inda aka fara ƙaddamar da aikin, za a gina titi mai tsawon kilomita 7.5 daga Mil Goma zuwa Yankatsari, sai kuma milomita 7.5 daga Rijiyar Gwangwan, wanda aikin na su zai ci Naira biliyan 2.6.”

People are also reading