Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Nijar, an Yi Hasashen Halin da Za a Shiga a Afrika
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum
Kasar Niger - Biyo bayan bukatar da kasar Nijar ta yi, Amurka ta fara janye sojojinta da suka kafa sansani a kasar.
Nijar ta nuna kin amincewa da cigaba da zaman sojin Amurka a yankin ne tun bayan juyin mulki da sojoji suka yi a bara.
Jaridar Premium Times ta fitar da hasashe kan yadda lamarin tsaro zai cigaba da kasancewa a yankin bayan fara tafiyar sojojin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasar Nijar ta kasance cikin wuraren da Amurka ta kashe $110m wajen gina sansanin soji domin yaki da musu ta'addanci a Afrika.
Sai dai Amurka ta fara janye sojojin ta a ranar 7 ga watan Yuni biyo bayan bukatar hakan da kasar Nijar ta yi wanda a yanzu saura sojin Amurka 6000 a kasar.
Kasar Amurka ta ce janye sojojin na cikin abubuwan da suka tattauna kuma suka fahimci juna da sojojin kasar Nijar.
Ta kara da cewa dama sun tattauna kan yadda za su kammala janye sojojinsu daga Nijar zuwa ranar 15 ga watan Satumba mai zuwa, rahoton Voice of America.
Biyo bayan fara ficewar sojojin Amurka a Nijar, an fara bayyana yadda lamarin tsaro zai kasance a yankin yammacin Afrika.
Duk da ana ganin Amurka za ta iya daukan sabon mataki na jigbe sojinta a wata ƙasa, masu hasashe sun ce za a zuba ido a ga yadda jami'an tsaron yankin za su iya yakar yan ta'adda su kaɗai.
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin sojojin juyin mulkin Nijar sun bayyana cewa hamɓararren shugaban kasa, Mohamed Bazoum ba zai dawo kan mulki ba.
Janar Abdulsalami Abubakar, ɗaya daga cikin jagororin wakilan ECOWAS shi ne ya bayyana haka bayan ya gana da Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine.
Asali: Legit.ng