Home Back

Adadin waɗanda ‘yan ta’adda ke kashewa ya ragu daga mutum 2600 a wata, zuwa mutum 200 a wata – Ribadu

premiumtimesng.com 2024/5/20
Adadin waɗanda ‘yan ta’adda ke kashewa ya ragu daga mutum 2600 a wata, zuwa mutum 200 a wata – Ribadu

Nuhu Ribadu, Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Musamman a Fannin Tsaro, ya bayyana cewa adadin waɗanda ke mutuwa a musabbabin hare-haren Boko Haram da ‘yan Najeriya ya ragu matuƙa sosai a ƙasar nan, daga mutum 2,600 a wata zuwa mutum 200 a wata.

Ribadu ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai yayin taron Hanyoyin Daƙile Ta’addanci a Afirka, wanda aka fara a Abuja a ranar Litinin.

Taron dai Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro (ONSA), Nuhu Ribadu ne ya shirya shi, tare da haɗin guiwa da Ofishin Daƙile Ta’addanci na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ribadu ya ce wannan gwamnati na samun gagarimar nasara sosai a fannin ƙoƙarin da ake yi na daƙile ta’addanci.

Ya ce hakan na ƙara tabbatuwa ne bisa la’akari da rayuwar da ake samu na yawan adadin mutanen da ke rasa rayukan su a kullum dalilin ta’addanci da hare-haren ‘yan bindiga.

Ya ce gwamnati na ci gaba da aikin daƙile hanyoyin da ‘yan ta’adda ke samun muggan makamai, ta hanyar toshe ƙofofin da makaman ke isa gare su.

Akwai Muggan Makamai Sama Da Miliyan 3 A Hannun Mugaye A Cikin Najeriya:

Ribadu ya ce aƙalla akwai makamai sama da miliyan 3 a hannun mugayen mutane a faɗin Najeriya.

“Aiki kam muna aiki wurjanjan. Kuma ina jin mun yi ƙoƙari sosai.

“Wasu dalilan da za su iya zama shaida ko hujja cewa muna matuƙar ƙoƙari, shi ne yadda a yanzu har Naira miliyan 5 ‘yan ta’adda ke sayen bindiga guda ɗaya, saboda ƙarancin ta da yadda ta ke wahalar samu. Amma a baya ba ta wuce Naira 500,000.00 a hannun su.

“Kuma duk waɗanda muka ƙwace, lalata su ake yi,” inji Ribadu.

Ya ce jama’a ba su sani ana samun wannan gagarimar nasarar, saboda gwamnati ta zaɓi ta yi shiru, ta daina yayata ayyukan da ta ke yi, musamman ci gaban da ake samu wajen daƙile matsalar tsaro.

People are also reading