Home Back

Sin Ta Cimma Wasu Sakamako Na Hadin Gwiwa Tare Da Kasashen GCC

leadership.ng 2024/6/29
Sin Ta Cimma Wasu Sakamako Na Hadin Gwiwa Tare Da Kasashen GCC

Kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf ko GCC a takaice, kungiyar siyasa da tattalin arziki mafi girma ce a yankin Gulf na daular Larabawa.

Daga ranar 23 zuwa ranar 24 ga watan nan na Mayu, an gudanar da dandalin tattaunawar hadin gwiwar masana’antu da zuba jari, na Sin da kasashe mambobin kungiyar ta GCC, a birnin Xiamen dake lardin Fujian.

Game da hakan, hukumar raya kasa da yin gyare gyare ta kasar Sin ta nuna cewa, dandalin tattaunawar na wannan karo ya cimma wasu sakamako masu amfani.

Bisa alkaluman baya bayan nan da aka fitar, a shekarar bara, yawan cinikin bangaren Sin da na kasashen GCC ya kai dalar Amurka biliyan 286, kuma Sin ta ci gaba da zama abokiyar cinikayyar GCC mafi girma.

Dandalin tattaunawar na wannan karo ya zabi misalai guda 47, daga sakamakon hadin gwiwa mafiya kyau don baje kolinsu, ta yadda za a kai ga kara karfafa damar hadin gwiwa.

Yayin gudanar da dandalin tattaunawar, hukuamr raya kasa da yin gyare gyare ta kasar Sin, ta fitar da ajandar ministoci game da karfafa hadin gwiwar masana’antu, da zuba jari na Sin da kasashen GCC, tare da manyan kasashen GCC guda shida. A nan gaba kuma, bangarorin za su karfafa shirin aiwatar da burikan su da gudanar da manufofinsu, da ba da cikakkun fa’idodinsu masu dacewa, da kuma bunkasa ci gaba mai inganci na masana’antu, da hadin gwiwar saka hannun jari. (Safiyah Ma)

People are also reading