Home Back

Juventus da Bayern na rububin Lookman, ina makomar Ten Hag a United ?

bbc.com 6 days ago
Ademola Lookman

Asalin hoton, SUPER EAGLES

Bayern Munich ta yi tayin karshe na neman dan wasan Fulham Joao Palhinha, West Ham za ta iya komawa zawarcin Max Kilman, yayin da Barcelona da PSG ke son dan wasan Manchester City Julian Alvarez.

Bayern Munich ta yi tayin karshe tsakanin fan miliyan 38-39 kan dan wasan Fulham kuma dan wasan tsakiya na kasar Portugal mai shekara 28 Joao Palhinha, wanda tuni ya amince da kulob din na Jamus. (Sky Sports Germany)

West Ham tana son biyan fan miliyan 35 don siyan dan wasan bayan Wolves na Ingila Max Kilman amma a shirye suke su duba da yadda Wolves din ta dakea kan farashin da ta sanya na £45m kan dan wasan mai shekaru 27. (Guardian)

Fulham na shirin tsawaita kwantiragin dan wasan gaban Brazil Willian, mai shekara 35, da dan wasan Jamaica Bobby De Cordova-Reid, mai shekara 31, ko da bayan kwantiraginsu da kulob din ya kare ranar Litinin. (Standard)

Ana samun ci gaba a tattaunawa tsakanin Manchester United da kocinta Erik ten Hag game da sabunta kwantaraginsa, kuma an ci gaba a wannan makon. (Sky Sports)

Chelsea ta dage kan farashin da ta sanya na fam miliyan 37 kan dan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku, duk da cewa AC Milan da Napoli na fatan farashin dan wasan mai shekaru 31 zai yi kasa a lokacin bazara. (Gianluca di Marzio)

Barcelona da Paris St-Germain na fatan shawo kan dan wasan Argentina Julian Alvarez, mai shekara 24, idan ya bar Manchester City a bazara. (Cut Offside)

Har ila yau AC Milan na zawarcin dan wasan gaban Ingila Tammy Abraham, mai shekara 26, wanda kwantiraginsa zai kai 2026 da Roma. (La Gazzetta dello Sport)

Juventus na sa ido kan dan wasan gaban Atalanta Ademola Lookman, yayin da ita ma Bayern Munich ke harin dan wasan mai shekaru 26, haka kuma kungiyoyin Premier da dama suna sha'awar dan wasan na Najeriya. (Mail)

Bayern Munich na tattaunawa da dan wasan baya na kasar Jamus Jonathan Tah daga Bayer Leverkusen kuma kungiyoyin biyu na dab da kulla yarjejeniya da dan wasan mai shekaru 28, wanda ya rage shekara daya a kwantiraginsa. (Sky Sports Germany)

Newcastle United tana da kwarin gwiwar cewa dan wasan gaban Sweden Alexander Isak, mai shekara 24, zai rattaba hannu kan sabon kwantiragi a bazara, a yayin da Chelsea ke zawarcinsa. (Givemesport)

Da wuya Barcelona ta nemi dan wasan baya na Bayern Munich na Jamus Joshua Kimmich, duba da yadda ake ganin dan wasan Everton na Belgium Amadou Onana, mai shekara 22, da kuma dan kasar Spain Mikel Merino mai shekaru 28, wanda ke taka leda a Real Sociedad ne suka fi dacewa da salon taka leda na kungiyar. (Mundo Deportivo)

Tottenham na zawarcin dan wasan Leeds Archie Gray, mai shekara 18, yayin da kungiyoyi a Spaniya da Jamus suka sa masa ido. (Talksport)

Everton ne kulob na baya-bayan nan da ke nuna sha'awar daukar dan wasan Hull dan kasar Ingila Jaden Philogene, mai shekara 22. (Echo)

Southampton na tattaunawa da kocinta Russell Martin game da tsawaita kwantiraginsa bayan da ya jagorance su zuwa sake komawa gasar Premier a karon farko. (Atletic)

People are also reading