Home Back

Tinubu ya ƙirƙiro Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi

premiumtimesng.com 2024/8/22
GARGAƊIN TINUBU GA TSAGERUN KUDU DA NA AREWA: ‘Za mu tarwatsa duk mai neman tarwatsa Najeriya’

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙirƙiro Ma’aikatar Bunƙasa Kiwon Dabbobi, wadda a Turance aka raɗa wa suna Ministry of Livestock Development.

Wannan bayani ya fito ne daga Fadar Shugaban Ƙasa, a ranar Talata, yayin ƙaddamar da Kwamitin Farfaɗo da Albarkatun Kiwon Dabbobi na Ajandar Fata Nagari Lamiri, wato Renewed Hope.

Ma’aikatar za ta maida hankali ne wajen bunƙasa kiwo da kuma cin moriyar tattalin arzikin da ya jiɓinci kiwon dabbobi, sai kuma ƙoƙarin kawo ƙarshen kashe-kashen baƙin makiyaya da manoma.

Tinubu ya ce shi ne zai kasance Shugaban Kwamitin Farfaɗo da Albarkatun Kiwon Dabbobi, yayin da tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, Attahiru Jega zai kasance Shugaban Kwamiti na 2.

Tinubu ya ce a duk lokacin da bai samu sukunin zaman kwamiti ba, to Jega ne zai jagoranci zaman kwamitin.

People are also reading