Home Back

Binciken Ma'aikatar Ministan Tinubu Ya Sanya EFCC Ta Kwato N32bn

legit.ng 2024/5/19
  • Hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta yi ƙarin haske kan binciken da take yi a ma'aikatar jinƙai da yaƙi da fatara
  • Hukumar EFCC ta yi nuni da cewa ya zuwa yanzu binciken ya sanya ta ƙwato N32bn, $445,000 da aka wawushe daga ma'aikatar
  • Kakakin hukumar mai yaƙi da cin hancin, Dele Oyewale, ya bayyana hakan a ciikim wata sanarwa da ya fitar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta ce ta ƙwato N32.7bn da $445,000 da aka wawushe a ma'aikatar jinƙai da yaƙi da fatara.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a shafin X da kakakinta, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Lahadi, 14 ga watan Afirilun 2024.

Hukumar EFCC ta kwato N32bn
Binciken EFCC ya sanya ta kwato N32bn a ma'aikatar jinkai Hoto: EFCC Asali: UGC

EFCC ta fito ta bayyana hakan ne bayan abin da ta kira yadda ake ta yawan maganganu kan binciken da take yi a ma'aikatar jinƙai da yaƙi da fatara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oyewale ya yi bayanin cewa a farkon binciken da hukumar ta fara, ta gayyato tsofaffi da dakatattun jami'an ma'aikatar domin ji daga bakinsu.

Wane bincike EFCC ke gudanarwa?

A cewar kakakin na EFCC, hukumar ta kuma fara binciken wasu ayyukan zamba da suka haɗa bashin da aka ciyo daga bankin duniya, kuɗaɗen Covid-19 da kuɗaɗen da aka karɓo na Abacha waɗanda aka ba ma'aikatar domin rage raɗaɗin talauci.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"A farkon fara bincike, an gayyato tsofaffi da dakatattun jami'an ma'aikatar jinƙai, kuma binciken da ake yi kan zargin zamba ya sanya ya zuwa yanzu an ƙwato N32.7bn da $445,000."
"Binciken kuma ya bankaɗo jami'an ma'aikatar masu yawa waɗanda ake zargin da hannunsu wajen yin sama da faɗi da kuɗaɗen."
"Yana da kyau a bayyana cewa binciken hukumar ba ana yinsa ba ne kan wasu mutane. EFCC na binciken ayyukan zamba ne masu yawa da aka aikata. Bankuna da ke hannu a ciki na fuskantar bincike."

Tsohon minista ya kai ƙarar EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan makamashi da ƙarafuna, Olu Ogunleye, ya shigar da ƙara kan hukumar EFCC a gaban kotu.

Tsohon ministan ya ɗauki wannan matakin ne.bayan hukumar ta wallafa sunansa a cikin mutanen da ake nema.

Asali: Legit.ng

People are also reading