Aliko Dangote Zai Gina Wani Sabon Kamfanin Siminti a Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Shahararren dan kasuwa kuma mai arzikin Afrika na daya, Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin gina kamfanin siminti a jihar Gombe.
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana haka ne yayin bikin auren 'yar Alhaji Umaru Kwairanga a jihar Gombe.
Mai taimakawa gwamnan jihar Gombe a harkar yada labarai, Isma'ila Uba Misilli ya fitar da sanarwa a shafinsa na Facebook cewa Dangote ya ce zai kafa kamfanin ne lura da yadda al'amuran kasuwanci ke bunkasa a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara kuma da cewa gwamnan jihar ya samar da yanayi mai kyau da zai taimakawa kasuwanci wurin habaka da kuma irin yadda jihar ke da sinadarin hada siminti sosai.
Dangote ya tabbatar da cewa idan suka fara hada siminti a jihar Gombe akwai yiwuwar farashin siminti zai sauka a yankunan da su ke kewaye da Gombe.
Za a samu wannan rangwame ne saboda rage nisan jigilar simintin da za a samu.
A wani rahoton kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe ta sanar da dokar sharar gama gari da za a rika yi duk ranar Asabar din karshen wata a fadin jihar
Dokar zata fara aiki ne a karshen watan Afrilu kuma za a rika daukan awa biyu ana gudanar da ita ba tare da barin zirga-zirgar al'umma ba
Gwamnatin ta yi kira ga daukacin al'ummar jihar da su yi iya kokari wurin bada hadin kai ga hukumomi domin tabbatar da tsaftace jihar baki daya
Asali: Legit.ng