Home Back

Ukraine na neman goyon bayan kasashen duniya don samun zaman lafiya a kasar

bbc.com 2024/7/3
Volodymyr Zelensky

Shugaba Zelensky na Ukraine na Switzerland domin halartar taron kwanaki biyu a kan yadda za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya a kasarsa.

Gwamman shugabannin kasashen duniya ne ake kyautata tsammanin za su halarci taron, to amma ba a gayyaci Rasha.

Shugaba Putin na Rasha ya ce Rasha za ta amince ta halarci taron zaman lafiyar ne bisa sharadin cewa Ukraine za ta yarda ta mika mata wasu yankuna hudu nata tare da alkawarin cewa ba za ta shiga ta zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO ba.

Tuni dai shugaba Zelensky ya yi watsi da bukatar Rashan.

Ana kyautata zaton cewa a yayin taron za a bullo da wasu hanyoyi na tabbatar da zaman lafiya a kasar wadda Rasha ta mamaye tsawon watanni 28 da suka wuce.

Wannan dai wani muhimmin taro ne ga Ukraine, to amma duk da haka akwai manyan kasashen duniya da suka kauracewa taron kamar China.

’Yan siyasa a Ukraine na ganin duk wanda ya halarci taron na daga cikin mutumin da ke son ganin an samar da zaman lafiya a kasarsu da yaki ya dai-dai ta.

Duk da wannan taro da za a fara, har yanzu Rasha bata fasa kai hare-hare ba, inda a baya-bayannan ta kai manyan hare hare arewacin Ukraine kusa da Kharkiv, inda suka fada kan gidajen jama’a da kuma tashoshin lantarki a yankin.

Wani dan majalisar dokokin Ukraine Oleksandr Merezhko, ya ce yana da matukar muhimmanci a samar da wani tsari bisa dokokin shari’a domin dorewar zaman lafiya a Ukraine.

Ya ce,”Idan ana so a cimma wannan manufa kuwa sai an yi la’akari da wasu muhimman manufofi 10 da Zelensky ya gabatar tun a baya da suka hada da tabbatar da cikakken ‘yancin Ukraine.”

Dan majalisar dai na bayani ne a kan wasu shawarwari da Zelenksy ya gabatar a karshen 2022, inda ya bukaci a tursasawa Rasha ta mayar musu da yankunan da ta mamaye.

Yanzu Ukraine na son samun goyon bayan kasashe da dama a kan wannan manufa ta ta.

Shugaban Amurka Joe Biden bai samu damar halartar taron ba sai dai wakili abin da bai yi wa Mr Zelensky dadi ba.

Sannan kokarinsa na ganin ya samu goyon bayan wasu kasashen ba lallai ya yi nasara ba.

Kasashe irinsu India da Brazil da kuma China ba su halarci taron ba kuma babu wakilci.

Tuni jami’an Rasha suka ce taron bashi da wani muhimmanci.

People are also reading