Home Back

Zwayer ne zai busa wasan Ingila wanda aka taɓa zargi da cogen tamaula

bbc.com 2024/8/25
Felix Zwayer

Asalin hoton, Getty Images

Raflin Jamus, wanda Jude Bellingham ya taɓa zargi da cogen wasa, shi ne zai busa daf da karshe tsakanin Ingila da Netherlands ranar Laraba a Euro 2024.

Felix Zwayer, mai shekara 43, shi ne zai ja ragamar alkalai daga Jamus da za su busa karawar ta daf da karshe.

A shekarar 2021, lokacin da Bellingham ke Borussia Dortmunt an ci tarar sa £34,000 bisa la'akari da cewar an taɓa dakatar da alkalin kan cogen wasa.

An dakatar da Zwayer wata shida a 2005, bayan da aka bincike shi kan karɓar na goron £250 daga wani jami'i, Robert Hoyzer.

Daga baya aka dakatar da Hoyzer daga shiga sabgogin tamaula har bayan rayuwarsa.

Bellingham ya yi kalamai kan alkalin wasan, bayan tashi karawar da Dortmund ta yi rashin nasara a hannun Bayern Munich da cin 3-2.

A karawar ce raflin ya bai wa Bayern fenariri, amma ya hana Dortmund, inda a lokacin Bellingham yana da shekara 18..

Ɗan kwallon Real Madrid na taka rawar gani a tawagar Ingila a Euro 2024, wanda ya ci Slovakia ƙwallo da cin fenariti a wasa da Switzerland.

Ya kuma ci Serbia a wasan cikin rukuni na uku a gasar ta cin kofin nahiyar Turai ta bana.

People are also reading