Home Back

Jigon PDP Ya Jero Ministoci 5 da ya Kamata Tinubu Ya Yi Waje da Su a Gwamnatinsa

legit.ng 2024/7/2
  • Yayin da ake kiran Shugaba Bola Tinubu ya sallami wasu daga cikin Ministocinsa, jigon PDP ya jero wadanda suka fi dacewa
  • Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar ya lissafo Ministoci biyar da ya kamata Tinubu ya sallama saboda rashin yin katabus
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban ya sha alwashin sallamar duk wani Minista da ya gaza yin wani abu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar PDP, Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar ya jero Ministocin da ya kamata Bola Tinubu ya kora a gwamnatinsa.

Abdul-Aziz ya bayyana cewa akwai Ministoci da dama da ba su tabuka komai ba yayin da Tinubu ya cika shekara daya a kan mulki.

Jigon PDP ya bayyana haka a yau Talata 4 ga watan Yuni a shafinsa na X inda ya jero sunayen Ministoci guda biyar da suka gaza.

"Sunayen Ministocin Tinubu guda biyar da ba su tabuka komai ba a gwamnatinsa."
"1. Ministan Matasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Ministan Makamashi
3. Ministan Albarkatun Ruwa
4. Ministan Tsaro
5. Ministar Harkokin Mata."

- Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar

Wannan martani na jigon PDP na zuwa ne yayin da ake yawan kiran Tinubu da ya sallami wasu daga cikin Ministocinsa.

Shugaba Tinubu da kansa ya ce zai sallami duka wadanda basu tsinana komai ba a cikin shekara daya da ya yi a gwamnati.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da kungiyar Arewa Consultative Forum a birnin Abuja a makon jiya.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading