Home Back

Sojojin Najeriya Za Su Tafi Maƙwabciyarta Domin Wanzar da Zaman Lafiya, an Jero Dalilai

legit.ng 2024/7/1
  • Sojojin Najeriya za su cilla kasar Gambia domin taimaka mata wurin wanzar da zaman lafiya da kare lafiyar al'umma
  • Dakarun akalla 197 ne aka horas domin sanin aikin da za su je yi a kasar da ke fama da matsalolin tsaro daban-daban
  • Wannan matakin na zuwa ne yayin da Najeriya ke cikin tsananin rashin tsaro na garkuwa da mutane da ta'adanci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da shirin taimakawa kasar Gambia da dakaru.

Hukumar ta tabbatar da tura sojoji 197 Gambia domin wanzar da zaman lafiya yayin da suke fama da matsalolin tsaro.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban bangaren ayyuka a hukumar, Manjo-janar, Boniface Sinjen ya fitar, cewar Punch.

Boniface ya hakan yana daga cikin hobbasan shugaban hafsan sojoji, Laftanar-janar, Taoreed Lagbaja domin taimakon kasashen duniya da dakaru.

Ya ce an basu horaswa na musamman da koyar da su dabarun wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An shirya ku domin kare lafiyar fararen hula, an koyar da ku hadin kai da shugabanci da kuma kiyaye al'adu domin samun nasara kan abin da kuka je yi."
"Kun samu horaswa domin samar da zaman lafiya a kowace irin al'umma da kuma kiyaye dokar kasa da mutunta ƴancin ɗan Adam."

- Boniface Sinjen

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading