Home Back

CBN Ya Hakura, Ya Fasa Karbar Kudaden da Ya Yi Niyya Wajen Ajiya a Banki

legit.ng 2024/5/19

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Babban bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan kasuwanci su dakatar da karbar la'adar ajiya har sai zuwa watan Satumba.

Bankin ya bayar da wannan umarni ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Adetona Adedeji, daraktan sa ido kan harkokin bankuna.

CBN ya dakatar da tsarin cirar la'ada a kudaden ajiya
CBN ya dakatar da karbar la'ada a kudaden ajiya Hoto: @cenbank Asali: UGC

Hakan ya biyo bayan zanga-zangar da abokan cinikin wasu bankunan ajiya suka yi na nuna adawa da cire kuɗaɗen, wanda aka dawo da shi a ranar 1 ga watan Mayu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Za a riƙa cirar kaso 2% cikin 100% na kuɗaɗen ajiyar ɗaiɗaikun mutane da suka kai sama da N500,000, yayin da masu asusun kamfani za a cire musu kaso 2% cikin 100% na kuɗaɗen ajiya da suka kai sama da N3m.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, a cikin sanarwar babban bankin na CBN ya fitar, ya ba da umarnin a dakatar da cirar kuɗin na tsawon watanni uku masu zuwa.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Babban bankin Najeriya (CBN) ya ƙara wa'adin dakatar da karɓar la'adar 2% da 3% da ake yi a baya kan kuɗaɗen ajiya har sai zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024."

Babban bankin ya umarci cibiyoyin hada-hadar kuɗi da su ci gaba da karɓar duk wasu kuɗade daga jama’a ba tare da cirar wani kaso ba har zuwa ƙarshen watan Satumba.

Asali: Legit.ng

People are also reading