Home Back

Yar’adua ya maye gurbin Ningi a matsayin shugaban kungiyar Sanatocin Arewa

premiumtimesng.com 2024/4/29
Ƙanin Umaru ‘Yar’Adua, Abdu Soja ya lashe kujerar Sanatan Katsina ta Tsakiya da jiɓin goshi

An nada Abdulaziz Yar’adua, Sanata mai wakiltar Katsina ta tsakiya a matsayin shugaban kungiyar Sanatocin Arewa (NSF).

Kungiyar ta kuma nada Mohammed Monguno, Sanata mai wakiltar Borno ta Arewa a matsayin sakataren yada labaranta.

An nada sanatocin biyu ne a ranar Laraba bayan murabus din Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi a matsayin shugaban kungiyar.

Monguno, lauya ne ya maye gurbin Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu, Summaila Kawu, a matsayin mai magana da yawun kungiyar.

Sanata Yar’adua, da kanin marigayi shugaba Umaru ‘Yar’aduwa, a jawabinsa, ya bayyana jin dadinsa ga takwarorinsa da suka bashi wannan matsayi.

Ya kuma tabbatar da cewa shugabancinsa zai fifita muradun kasa da ci gaban yankin Arewa.

Sanatan ya yi alkawarin hada kai da takwarorinsa domin dorewar hadin kai da ci gaban kasa.

Babban makasudin kafa wannan kungiya shine shi ne inganta muradun Najeriya da farko sai ci gaban arewa ta hanyar hada hannu da da abokan aikinmu wato sanatoci na kudu da hada hannu da bangaren zartaswa na gwamnati domin ganin an fuskanci kalubalen da yankin ke fama da su an kuma warware su.

 
People are also reading