Home Back

NAHCON Ta Gargadi Alhazai Kan Shiga Da Haramtattun Kayayyaki Saudiyya

leadership.ng 2024/7/1
NAHCON Ta Gargadi Alhazai Kan Shiga Da Haramtattun Kayayyaki Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), ta sake gargadin maniyyata aikin hajjin 2024 da su guji safarar haramtattun kwayoyi da goro da sigari ko sauran abubuwan da aka haramta zuwa kasar Saudiyya. 

Hukumar ta ce Saudiyya kasa ce da ke amfani da dokokin addini da al’adu kuma tana da tsauraran dokoki kan fataucin miyagun kwayoyi tare da hukuncin kisa ga duk wanda ta samu da laifin karya dokar.

NAHCON ta yi wannan gargadi ne cikin wata sanarwa mai dauke dauke da sa hannun mataimakiyar daraktan hulda da jama’a, Fatima Sanda Usara a ranar Alhamis a Abuja.

NAHCON ta tunatar da maniyyatan cewa manufar tafiyarsu zuwa Saudiyya ibada ce, don haka kada su shagaltu da ayyukan da za su keta alfarmar hajjinsu inda ta ce hajji lokaci ne na addu’o’i da ya kamata a tunkare shi cikin girmamawa da mutunta dokoki da al’adun kasar mai masaukin baki.

Ta shawarce maniyyatan da su rika lura da jakunkunansu a tashoshin jiragen sama don gujewa dasa kayan da aka haramta a cikin kayansu ba tare da saninsu ba, kana ta bukaci alhazai da su kare martabarsu da ta kasa, inda ta yi gargadin cewa duk mutumin da aka kama yana safarar kayayyakin da aka haramta ba wai kawai ya jawo wa kansa abin kunya ba, har ma da zubar da mutuncin al’ummarsa.

Hukumar ta kuma yi kira ga hukumomin alhazai na jihohi da su hada kai da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) da sauran hukumomin da ke da alaka da su wajen ganin an kama mutanen da ke shirin safarar kayayyakin da aka haramta a Saudiyya don gujewa abin kunya da kuma jinkirin da ba a bukata yayin tantance su.

People are also reading