Home Back

Bobrisky: Kotu Ta Dauki Mataki Kan Fitaccen Ɗan Daudu a Legas, Ya Roki Alfarma

legit.ng 2024/5/17
  • Yayin da ake ci gaba da shari'ar ɗan daudu, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky, kotu ta umarci garkame shi a gidan kaso
  • Babbar Kotun Tarayya ta sanya 9 ga watan Afrilu a matsayin ranar yanke wa Bobrisky hukunci bayan ya amince da laifuffukansa
  • Wannan na zuwa ne bayan hukumar EFCC ya cafke Bobrisky a jiya Alhamis 4 ga watan Afrilu a jihar Legas kan wasu zarge-zarge

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Babbar kotun Tarayya da ke jihar Legas ta saka ranar yanke hukunci kan ɗan daudu, Idris Okuneye.

Kotun ta tanadi hukunci kan ɗan daudu, Bobrisky domin yanke masa hukuncin a ranar 9 ga watan Afrilu.

Kotu da dauki mataki kan shari'ar ɗan daudu, Bobrisky a Legas
Kotu ta garkame ɗan daudu, Bobrisky yayin da ta saka ranar yanke masa hukunci. Hoto: @bobrisky222. Asali: Instagram

Wane mataki kotun ta yanke kan Bobrisky?

Bobrisky ya amince da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi kansa guda hudu bayan hukumar EFCC ta cafke shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin kotun ya umarci ci gaba da tsare Bobrisky a gidan kaso har zuwa ranar yanke hukuncin, a cewar Daily Trust.

Tun farko, kafin fara gudanar da shari'ar, alkalin kotun ya umarci Bobrisky ya cire hijabi da ya lullube fuskarsa wanda ya bi umarnin nan take.

Lauyan hukumar EFCC, Sulaiman Sulaiman ya roki kotun ta cire tuhume-tuhume guda biyu daga cikin shida da ake tuhumar Bobrisky, cewar Channels TV.

Sulaiman ya ce sun yi yarjejeniya da wanda ake zargi kan cewa za su rage guda biyu daga cikin tuhume-tuhume shida zuwa guda hudu.

Bobrisky ya nemi afuwa a gaban alkali

Alkalin kotun, Mai Shari'a, Awogboro ya janye tuhume-tuhumen guda biyu inda ya umarci a karanto sauran laifuffukan guda hudu.

Bayan karanto laifuffukan, Bobrisky ya amince da aikata su inda ya bukaci a yi masa afuwa ba zai sake aikata laifin ba.

Ya ce ya na da mabiya sun fi miliyan biyar, bai san da dokar ba ko kuma hakan aikata laifi ne inda ya ce wannan shi ne karon farko da ya yi laifin.

EFCC ta kama fitaccen ɗan daudu, Bobrisky

A baya, mun baku labarin cewa Hukumar EFCC ta cafke fitaccen ɗan daudu a Najeriya, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky a jihar Legas.

Hukumar ta dauki matakin ne yayin da ake zargi Bobrisky da watsa takardun naira da kuma cin mutuncinta wanda ta sabawa dokar kasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

People are also reading