Home Back

ƘARIN ALBASHIN ALƘALAI: An yi wa alƙalai ƙarin nunki uku na albashi da alawus-alawus

premiumtimesng.com 2024/10/5
ZAMAN SHARI’AR JAYAYYA DA TINUBU: Kotu ta ce lauyoyi su daina ƙaƙale-ƙaƙale, mai hujja ya baje ta a faifai kawai

Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin ƙarin albashin manya da ƙananan alƙalai na tarayya da na jihohi har da na majistare-majistare.

A ƙarƙashin ƙudirin wanda aka amince da shi a ranar Alhamis, za a yi masu ƙarin kashi 300% bisa ɗari, wato zai nunka sau uku kenan.

Sabon tsarin biyan albashin dai ya amince a gabza wa Cif Jojin Najeriya albashi da alawus na Naira miliyan 64 a shekara, sai kuma Naira miliyan 31.9 ya sayi kartsetsiyar mota.

Amincewar ta zo ne bayan Shugaban Kwamitin Alƙalai, Kotuna, ‘Yancin Bil’Adama da Harkokin Shari’u, Sanata Mohammed Monguno ɗan Yankin Barno ta Arewa ya gabatar da rahoton kwamitin sa.

Ƙudirin dai tun da farko Shugaban Ƙasa ne Bola Tinubu ya gabatar da shi ga Majalisar Dattawa, domin ta amince da ƙarin.

Ƙudirin ya yi maida albashin Babban Jojin Najeriya Naira miliyan 5.385, Alƙalan Kotun Ƙoli kuma kowanen su Naira miliyan 4.213, sai Babban Alƙalin Kotun Ɗaukaka Ƙara kuma Naira miliyan 4.478.

Alƙalan Kotunan Ɗaukaka Ƙara za a riƙa ba su albashin Naira miliyan 3.726 duk wata, sai Alƙalan Babbar Kotun Tarayya da sauran shugabannin kotuna za su riƙa karɓar Naira miliyan 3.527.

Idan za a tuna, makonni biyu da suka gabata, Cif Jojin Najeriya ya yi gargaɗin cewa, ‘a ƙara wa alƙalai albashi don kada su riƙa yi wa ‘yan Najeriya bahangurɓar shari’a’.

Babban Mai Shari’a na Ƙasa, wato Cif Joji ko Alƙalin Alƙalan Najeriya, Olukoyede Ariwoola, ya bayyana cewa idan ba a biyan alƙalai albashi da alawus yadda ya kamata, to fa ‘yan Najeriya ne za su cutu.

Ariwoola ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ranar Litinin, wanda taro ne na jin ra’ayin jama’a da Kwamitin Majalisar Dattawa mai Lura da Shari’a, Kotuna, ‘Yancin Bil’Adama da Ayyukan Shari’a ya shirya.

Ariwoola ya tura wakilci ne, inda Babban Jojin Jihar Barno, Kashim Zannah ya wakilce shi.

A jawabin sa, Cif Jojin Najeriya ya ce buƙatar a yi wa alƙalai ƙarin albashi da ƙarin alawus da sauran haƙƙoƙin su, abu ne mafi alheri ga ‘yan Najeriya. Domin idan ba a yi masu ba, to ‘yan Najeriya ɗin ne za su cutu.

“Idan ana biyan alƙalai haƙƙoƙin su da tsoka, to za su yi aiki tsakanin su da gaskiya. Amma idan ba su da albashi na kirki ko alawus da sauran haƙƙoƙi na kirki, to fa ‘yan Najeriya za su ɗanɗani bahangurɓar Shari’a.” Inji shi.

Cif Jojin na Najeriya ya misalta halin rashin albashi mai tsaka da alƙalan Najeriya ke fama da shi, wanda ya ce kamar marar lafiya ne da ke kwance mutu-kwakwai-rai-kwakwai, kuma ya na buƙatar ceton gaggawa.

“Masu girma Sanatoci, a taƙaice abin da muke cewa shi ne. Halin da alƙalan Najeriya ke ciki tamkar marar lafiya ne da ya kai gargara a asibiti, wanda ke buƙatar ceton gaggawa daga hannun likitoci.”

Daga nan ya jinjina wa kwamiti da ya shirya taron jin ta bakin waɗanda lamarin ya shafa.

Ya bayyana masu irin halin ƙuncin alƙalai da dama ke fuskanta a ƙasar nan.

Ya ce rabon da a yi wa alƙalai ƙarin albashi tun cikin 2007, tsawon shekaru 17 kenan.

Ministan Shari’a Lateef Fagbemi ya ce gwamnatin da ta gabata ta yi ƙoƙarin ƙara wa alƙalai albashi, amma sai ba a samu amincewa ba.

Ya ce a yanzu ya rubuta wa Shugaba Tinubu cewa a yi wa alƙalai ƙarin kashi 300% na albashin su. Wato mai ɗaukar albashin Naira 10,000, zai riƙa ɗaukar Naira 40,000 kenan, a misali.

People are also reading