Home Back

Jigilar Alhazai Zuwa Gida: ‘Hukumar NAHCON ba da wasa ta ke ba’, Alhazai sun yaba da aikin kwashe su zuwa Najeriya

premiumtimesng.com 3 days ago
Jigilar Alhazai Zuwa Gida: ‘Hukumar NAHCON ba da wasa ta ke ba’, Alhazai sun yaba da aikin kwashe su zuwa Najeriya

A ci gaba da kwashe Alhazan Najeriya zuwa gida Najeriya da ake yi, Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON ta kwashe Alhazai aƙalla 20,000 zuwa ƙasa Najeriya.

Bisa ga alƙaluman da hukumar ke fiddawa a kowacce rana na yawan Alhazan da ake kwashewa zuwa Najeriya A yau Talata, Alhazai sama 18,000 ne suka isa gida Najeriya.

Wannan aiki na kwashe alhazai yana tafiya cikin sauri ta yadda sauran Alhazan dake ƙasa kuma suke shirin komawa gida a Makka ke tofa albarkacin bakunansu game da yadda jigilar ke gudana.

Wasu alhazai da suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA a garin makka sun nuna jin daɗinsu game da yadda aikin ke gudana tare da yin fatan Allah ya maida kowa gidansa lafiya.

” A yadda aikin jigilar alhazai zuwa gida ke gidana a halin yanzu za mu iya cewa za a iya kammala kwashe Alhazan zuwa Najeriya cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

” Idan kuma ka lura, yadda shugaban hukumar ya ɗauko aikin sa tun daga zuwan Alhazai za ku gane cewa ba da wasa ya ke ba.

” Ya kammala aikin zuwa da Alhazai ƙasa mai tsarki awa 72 kafin lokaci, to haka nake gani za a kammala wannan ma cikin lokaci ƙalilan.” In ji wani Alhaji a garin Makka.

Ita ko wata Hajiya ƴar jihar Kaduna, cewa ta yi ɗokin ta koma gida shine kawai a gabanta.

” Ɗokin komawa gida shine ke damu na a halin yanzu. Amma yadda jigilar ke gudana, nan ba da dadewa ba zamu tafi muma. Na lura abin ba da wasa ake yi ba karkashin wannan sabon shugaban.

Hajiya Mairo ta ce “kama daga yadda ake kwashe kayan Alhazai a yi ga a da su zuwa kai su filin jirgi na Jedda, abin gwanin sha’awa, cikin tsari. Kana isa gida za ka iske kayan ka suna jiranka.

” Ni dai haka ƴan uwana da suka riga ni gaba suka rika cewa.

Da yawa daga cikin Alhazan bana sun ba NAHCON uzuri baya ga yaba mata ganin cewa wannan shine aikin Haji na farko da sabon shugabanta Jalal Arabi zai gudanar a matsayinsa na shugaban hukumar.

People are also reading