Home Back

RUƊANIN SARAUTAR KANO: Kwankwaso ya nemi Tinubu ya gaggauta hana ɓarkewar mummunar fitina a Kano

premiumtimesng.com 2024/6/30
KWANKWASO DA PETER OBI ZA SU YI ‘KOLABO’: Tabbas muna tattaunawar yiwuwar haɗewa don kada APC da PDP a zaɓen 2023 – Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma tsohon Ministan Tsaro, Rabi’u Kwankwaso ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu cewa ya gaggauta kawo ƙarshen ƙoƙarin da wasu na cikin gwamnatin sa ke yi da ke neman haddasa mummunar fitina a Kano.

Kwankwaso ya bayyana haka dangane da ruɗanin da ya biyo bayan rushe sarakuna biyar da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya naɗa da kuma naɗa Sarki Muhammadu Sanusi II kan mulkin da aka cire shi cikin 2020.

Kwankwaso ya shawarci Tinubu kada ya bari shugabannin APC su Abdullahi Umar Ganduje su yi amfani da jam’iyya mai riƙe da gwamnatin tarayya su balbala wutar fitina a Kano.

Kwankwaso ya ce Tinubu kada ya bari a haifar da ruɗanin da za a hana gwamna aikin sa wanda dokar ƙasa ta ba shi.

Ya ce batun naɗa Sarki ko tsige Sarki batu ne da doka ta damƙa hannun gwamnan Kano Abba Kabir-Yusif.

Ya ce dawo da tsigaggen Sarki a Kano da ba shi kariya da sojoji ke yi abu ne da ka iya jefa Kano cikin mummunan rikici.

Ya tunatar da Tinubu irin ɗauki-da-daɗin da ya yi da Gwamnatin Tarayya lokacin da ya na gwamnan Jihar Legas, kuma ‘yan Najeriya suka goyi bayan sa.

Kwankwaso ya ce to halin da aka jefa Kano ko ake neman jefa Kano, kamar irin yadda gwamnatin tarayya ta yi wa Tinubu ne lokacin ya na gwamnan Legas, kuma ya jajirce ya ƙi amincewa.

Kwankwaso ya yi wannan bayani cikin wata sanarwa da Malam Absulmalik Suleiman ya fitar a madadin sa, a ranar Asabar.

Dangane da halin da ake ciki a Kano, wakilin mu ya ruwaito Gwamna Abba, magoya bayan Sarki da cincirindon ‘yan Kwankwasiyya sun kwana tsaron Fadar Sarki Muhammadu Sanusi II.

Cincirindon magoya bayan Sarki Muhammadu Sanusi II da dafifin ‘yan Kwankwasiyya sun yini sun kwana tsaron Gidan Sarki Muhammadu Sanusi II, har zuwa wayewar safiyar Lahadi.

Shi kan sa Gwamna Abba Kabir-Yusif da ya yini a gidan cur har zuwa dare, ya koma gidan daidai ƙarfe 1:17 na dare.

Dafifin tsare fadar ya biyon bayan zargin da ake yi cewa jami’an tsaro na jiran samun wata ‘yar dama domin su shiga da tuɓaɓɓen sarki, Aminu Ado a cikin gidan.

Dama tun da rana magoya bayan Aminu Ado ke cewa sai cikin dare za su shiga su fito da Sarki Muhammadu Sanusi II, ko da tsiya, kamar yadda aka yi masa bayan cire shi a 2020.

Cikin masu irin waɗannan zafafan kalaman har da tsohon Kwamishinan Ayyuka na zamanin mulkin Abdullahi Ganduje, wanda Ganduje ya cire bayan samun saɓani, wato Magaji.

Dama kuma gamayyar rundunar tsaro a Jihar Kano, sun ce umarnin kotu za su bi, ba umarnin Gwamna Abba ba.

Akwai alamomi da ke nuna cewa shi kan sa Aminu Ado ya na fakon samun damar a shiga da shi cikin gidan Sarki da tsakar dare.

Wakilin mu ya ci karo da wani bidiyo inda tsohon Sarki ke tsaye a cikin dandazon magoya bayan sa, ga wani tsaye kusa da shi ya na bayanin cewa jami’an tsaro sun kusa zuwa domin a danna Fadar A shigar da Aminu komin dare. Shi ma ya nuna cewa a can za su kwana zaman jiran a je a tafi da Aminu zuwa fada.

Ɗimbin jama’a sun riƙa kai gudummawar ruwa, lemo mai sanyi da abinci daban-daban ga dandazon jama’ar da suka kwana su na tsaron Fadar Sarki Muhammadu Sanusi II.

Alamomi da kalaman da ke yawo a cikin gari da soshiyal midiya na nuni da cewa za a ɗauki tsawon kwanaki ana tsaron fadar, kafin a shawo kan rikicin.

Yayin da ake wannan dambarwa, har yanzu dai Fadar Shugaban Ƙasa ba ta ce komai ba.

Tun a ranar Asabar dai tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya ce gwamnatin tarayya ta karya dokar ƙasa ta shiga cikin ruguguwar sha’anin mulkin Kano. Ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya guji haddasa fitina a Kano.

Haka Majilisar Malaman Jihar Kano ta yi kakkausan suka da kira ga Shugaba Tinubu cewa matsalar Kano ba ta gwamnatin tarayya ba ce, ta gwamnatin Kano ce. Ta ce kada ya bari wasu daga waje su haddasa fitina a Kano.

Kungiyar Lauyoyi ta Jihar Kano, NBA ta yi Allah wadai da yadda ake amfani da sojoji a ruɗanin sarautar Kano.

Idan ba a manta ba, shi ma Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam, ya ce Gwamnatin Tarayya ta karya dokar ƙasa, inda a cikin dare aka kai tsohon sarki Aminu Ado cikin Gidan Nasarawa, wanda mallakar Gwamnatin Kano ne, ba da sanin Gwamnan Kano ko neman iznin sa ba.

People are also reading