Home Back

Gwamnatin Kano ta ce Aminu Ado ya fice daga Gidan Nasarawa za ta rushe bango, ta yi kwaskwarima

premiumtimesng.com 2024/7/2
Gina Jami’oi masu zaman kansu zai sa dalibai samun guraben Karatu – Sarkin Kano, Aminu Bayero

Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta fara aikin rushe katangar gidan Sarki na Nasarawa da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ke ciki, tana mai cewa “saboda ya lalace”.

Gidan Nasarawa dai ya na kusa daf da gidan Gwamnatin Jihar Kano, inda Gwamna Abba Kabir-Yusif ke gudanar da mulki, kuma ya ke zaune da iyalin sa.

Da yawan magoya bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da ‘yan Kwankwasiyya na ganin cewa ci gaba da zaman Aminu a gidan wata babbar barazana ce ga Gwamna Abba Gida-gida, wanda ɗan uwa ne na jini ga Aminu Ado da kuma Sarki Sanusi.

Ko a ranar Sallah rahotanni sun ce magoya bayan Aminu da ke tsaye a bakin hanyar Gidan Nasarawa sai da suka jefi kwanba ɗin motocin Gwamna Abba.

Gwamnatin ta kuma umarci Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar da ya fitar da Aminu Ado daga gidan bayan hukuncin kotu a ranar Alhamis, wanda ta yi iƙirarin cewa ya ba ta nasara a kan ɓangaren da suka shigar da ƙarar.

Kwamashinan Shari’a na Kano Haruna Isa Dederi ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar a Gidan Gwamnati, inda ya jaddada cewa bangon ƙaramin gidan Sarki da ke ƙwaryar birnin Kano ya lalace.

“Mun kammala shirye-shirye domin rushewa da kuma sake gina katangar da ta lalace nan take,” in ji shi.

Haka kuma wasu hotuna masu dishi-dishi da ke yawo a wasu shafukan zumunta, sun nuna cewa Aminu Ado ya fice daga cikin Gidan Nasarawa da tsakar daren Alhamis, kafin wayewar garin yau Juma’a.

Sai dai duk da akwai wani bidiyon da ke nuna ana ta tattara kayayyaki a gidan, har yanzu babu wata sanarwa daga ɓangaren gwamnati ko Aminu Ado da ke nuni da cewa ya fice daga gidan.

Idan kuma ya fice, har yanzu ba a ji inda ya ɓulla ba.

Tun farkon batarnaƙar sai da Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam ya ce Gwamnatin Tarayya da Aminu Ado sun karya doka, inda aka saukar da Aminu a Gidan Nassarawa, wanda mallakar Gwamnatin Kano ne, ba tare da sanar da Gwamna ko Gwamnatin Kano ba.

People are also reading