Home Back

Amurka ta saka takunkumin kan tsohon kwamandan Iran da ke takarar shugabancin kasar

rfi.fr 2024/6/26

Amurka ta kakkabawa daya daga cikin yan siyasar kasar Iran da ya shigar da takararsa a zaben shugabancin kasar takunkumin, saboda kasancewarsa a cikin rukunin masu aiki da Jagoran juyin juya hali Ayatollah Ali Khamenei, wanda Amurka ta zarge shi da keta hakokin bil Adam.

Wallafawa ranar: 01/06/2024 - 20:49

Minti 2

Ayatollah Mohammad Ali Movahedi Kermani Jagoran juyin juya halin kasar ta Iran
Ayatollah Mohammad Ali Movahedi Kermani Jagoran juyin juya halin kasar ta Iran AP - Vahid Salemi

Vahid Haghanian dan siyasa kuma daya daga cikin masu fada a ji a kasar ta Iran ya yi rajistar takararsa a yau Asabar a zaben shugaban kasa da aka shirya yi a karshen watan Yuni, Kamar sauran 'yan takara.

Matakin na Amurka ya zo a wani lokaci da yan kasar ta Iran ke ci gaba da nuna kiyaya ga manufofin Amurka,musaman ganin ta yada ta ke kokarin durkusar da siyasar kasar ta Iran a idanun Duniya.

Wasu daga cikin yan siyasar kasar ta Iran
Wasu daga cikin yan siyasar kasar ta Iran © Isna

Kalo ya koma bangaren majalisar kasar masu lura da kuma kare manufofin kasar ta Iran da za ta amince da takarar Vahid Haghanian,ƙungiyar masu ra'ayin mazan jiya na lauyoyi 12 waɗanda ke yin bitar duk masu neman kujerar shugabancin wannan kasa.

Magoya bayan siyasar kasar Iran
Magoya bayan siyasar kasar Iran AP - Vahid Salemi

Kamar marigayi shugaba Ebrahim Raïssi, Vahid Haghanian  ya kasance daga cikin mutanen da Amurka ta kakabawa takunkumin tun shekara ta 2019,hakan bai hana shi bayyana cewa ya na daga cikin mutanen da suka san  matsalolin kasar Iran "da kyau."

Ya ce ya kulla alaka ta kut-da-kut da manyan jami’an gwamnati “a cikin shekaru 45 da ya yi yana hidima a ofishin shugaban kasa. Za a gudanar da  zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Yuni bayan mutuwar Raïssi a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a ranar 19 ga watan Mayu.

People are also reading