Home Back

RIGIMAR MAFI ƘANƘANTAR ALBASHI: ‘Naira 100,000 ta yi kaɗan, ballantana Naira 62,000’ – Shugaban NLC

premiumtimesng.com 2024/7/1
Yajin Aikin NLC: Cin zalin Talaka ko amfani da Talaka don biya wa kai buƙata

Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa ko tayin Naira 100,000 matsayin mafi ƙanƙantar albashi Gwamnatin Tarayya ta yi wa ma’aikatan ƙasar nan, to kuɗin ya yi kaɗan, ballantana Naira 62,000.00
Ajaero ya bayyana haka a birnin Geneva na ƙasar Switzerland, inda ake taron Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya (ILO).

Ya ce kwamitin Gwamnatin Tarayya ya kai wa Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu Naira 62,000, sannan kuma ya ba shi Naira 250,000 wadda NLC ta ce haka zai kasance mafi ƙanƙantar albashi, domin ya duba.

“Saboda haka mu yanzu muna jiran jin ta bakin Shugaban Ƙasa ne.

“Ba za mu iya tafiya yajin aiki ba a yanzu, saboda muna jiran jin ta bakin Shugaban Ƙasa ne tukunna.

“Shugaban ƙasa ya lura akwai tazara sosai tsakanin 62,000 da 250,000. Amma dai muna jiran ta bakin sa.

“Ta yaya gwamnoni waɗanda ba su bayar da wata gudunmawar komai wajen tattalin arzikin Najeriya za su ce ba su iya biyan Naira 60,000 mafi ƙanƙantar albashi? To a ina shi Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya samu kuɗin da zai riƙa biyan Naira 70,000 mafi ƙanƙantar albashi, su kuma sauran su ce ba za su iya ba?”

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ajaero ya yi wannan bayani a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, a taron Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya (ILO), a birnin Geneva, wanda yanzu haka taron ke gudana.

PREMIUM TIMES Hausa ta ruwaito cewa ƙungiyar NLC da TUC sun yi fatali da ƙarin Naira 62,000, wanda suka ce mayunwaci ne za a bai wa wannan kuɗin, amma ba ma’aikatacin gwamnati ba.

People are also reading