Home Back

Kwaskwarimar Kundin Tsarin Mulki Zai Gyara Kura-kuren Da Aka Samu A Zaben 2023 – Abbas

leadership.ng 2024/4/28
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Shugaban majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, muhimman bangarori da kwamitin gyaran kundin tsarin mulki ke yin kwaskwarima zai gyara kura-kuren da aka samu a lokacin zaben 2023.  

Abbas ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi wajen kaddamar da kwamitin gyaran kundin tsarin mulki a Abuja. Ya ce akwai bukatar gyara wasu muhimman bangarori na tsarin mulki wanda majalisa ta dukufa wajen ganin an gyrasu domin karfafa harkokin shugabanci.

A cewarsa, wadannan bangarori suna da mutukar muhimmanci ga dimokuradiyyar Nijeriya da kuma tabbatar da abubuwan da tsarin shugabanci ke bukata ga ‘yan Nijeriya.

Ya ce an gabatar da kudurori daban-daban kan lamarin a tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai da ke da mutukar muhimmanci.

Shugaban majalisar ya bukaci kwamitin ya yi aiki kan kudurin majalisa ta 10 domin farfado da harkoki shugabanci a kasar nan.

Ya ce tuni dai majalisar take aiki kan tsarin gyaran kundin mulki da kuma lokacin da majalisar kasa ta amince da shi na kammala gyaran.

A bangare daya kuma, mataimakin shugaban majalisar wakilai kuma shugaban kwamitin gyaran kundin tsarin mulkiin, Hon. Benjamin Kalu ya ce za a samar da sabon tsarin kundin mulki kafin 2025.

Kalu ya ce za a bai wa dukkan ‘yan Nijeriya damar bayar da tasu gudummuwa wajen kokarin sake fasalin makoman Nijeriya a cikin gyaran kundin tsarin mulkin.

 
People are also reading