'Yan Bindiga Sun Hallaka Matashi Bayan Ya Kai Musu Kudin Fansa a Kaduna
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun harbe wani matashi ɗan shekara 27 mai suna Abba, bayan ya kai musu kuɗin fansa a jihar Kaduna.
Matashin ya kaiwa ƴan bindigan Naira miliyan 16 da babura uku domin sako wasu mutane tara da suka yi garkuwa da su a garin Jere da ke jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta ce ƴan bindigan sun mamaye wasu gidaje a Unguwar Iya da ke Jere a ranar 16 ga Afrilu, 2024, inda suka yi garkuwa da mutane tara tare da neman a ba su Naira miliyan 30.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin yankin, Shuaibu Hussaini, ya tabbatar da kashe Abba yayin da yake zantawa da wakilin jaridar ta wayar tarho a ranar Laraba.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar bayan matashin wanda da shi aka yi cinikin kuɗin fansan ya je kai Naira miliyan 16 da babura uku ga shugaban ƴan bindiga a wani wuri da ke yankin.
Ya ce shugaban ƴan bindigan bayan ya karɓi kuɗin fansa da baburan, sai ya ɗaure marigayin da igiya sannan ya buɗe masa wuta.
"Ɗaya daga cikin mutanen da aka sako cikin waɗanda aka sace ne ya ce shugaban ƴan bindigan ya yi iƙirarin cewa sun kashe Abba ne saboda ya yi musu tsaurin ido yayin ciniki kan kuɗin fansan."
"Sai a lokacin da wani ɗan uwansa ya yi ƙoƙarin sanin inda Abba yake bayan ya kai kuɗin fansan, sannan shugaban ƴan bindigan ya ce su je wani waje su ɗaiko gawarsa."
- Shuaibu Hussaini
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, bai ce komai ba kan lamarin.
Legit Hausa ta yi ƙoƙarin jin ta bakinsa kan lamarin, sai dai bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
A wani labarin kuma, kun ji cewa an tabbatar da mutuwar mutum shida yayin da wasu da dama kuma aka yi garkuwa da su a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki a jihar Kaduna.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a yankin Bauda da Chibiya a gundumar Maro da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng