Home Back

ABCON: Ƴan Kasuwa Sun Fara Sayen Dala a Ƙasa da N1,000, Suna Ɗora Ribar N40

legit.ng 2024/5/16
  • Alamun sauƙi na ta kara bayyana yayin da ƴan kasuwar musayar kuɗi suka fara sayen Dalar Amurka a N980
  • Shugaban ƙungiyar ƴan canji (ABCON), Aminu Gwadabe, ya bayyana cewa yanxu haka suna sayen Dala N980 su sayar da ita kan N1040
  • Ya yabawa gwamnatin tarayyar Najeriya da babban bankin CBN bisa matakan da suka ɗauka wanda ya dawo da darajar Naira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ƙungiyar ƴan canji na kasuwar bayan fagen (ABCON) ta bayyana cewa ƴan kasuwar musayar kuɗin sun fara sayen Dalar Amurka kan N980/1$.

ABCON ta kuma bayyana cewa ƴan canjin suna sayar da Dalar kan N1,020/$ ga kwastomomi bayan sun saya a N980/$ watau suna ɗora ribar N40 ne kacal.

Naira da Dala.
Yan canji sun fara sayen Dalar Amurka kan N980 a Najeriya Hoto: @Centralbank Asali: Getty Images

Shugaban ƙungiyar ABCON, Aminu Gwadebe, ne ya tabbatar da wannan ci gaban yayin da ya bayyana a cikin shirin kasuwanci na Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ƙara da cewa Nairq na ci gaba da ƙara daraja a kan Dalar Amurka fiye da yadda masu hasashe suka yi tsammani.

Gwadebe ya yabawa gwamnatin tarayya karƙashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da babban bankin Najeriya (CBN) bisa kokarin da suke yi har zuwa yanzu.

Ya ce wannan shi ne karo na farko a shekaru 15 da farashin Dala a kasuwar bayan fage ya fi arha fiye da farashin da ake musaya a kasuwar gwamnati.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Gwadabe ya ce yanzu hankalin kowa a kwance yake a kasuwar saboda raɗe-rafin da ke lalata lamarin babu shi a yanzu.

Shugaban ABCON ya. ce:

"A wurin mu muna sayen kowave Dala ɗaya a kan N980 kuma muna sayarwa a kan N1,020 yanzu haka. An samu ƙwarin guiwa."
"Yanzu haka muna da tarin kudaden waje da ‘yan kasashen waje ke shigowa da su saboda dimbin manufofin da CBN ya ɓullo da su waɗanda suka daidaita yada kuɗaɗen za su riƙa shigowa."

Ƙimar Dalar Amurka ta ƙara faɗuwa

A baya mun kawo muku rahoton cewa Bashir Ahmad ya ce ya samu sahihin bayanin cewa ana musayar Dala kan farashi ƙasa da N1,000 a wurin wasu ƴan canji a Najeriya

Ahmad, tsohon hadimin shugaban ƙasa a gwamnatin Muhammadu Buhari ya nuna kwarin guiwar cewa Naira za ta ci gaba da tashi.

Asali: Legit.ng

People are also reading