Home Back

Sarautar Kano: Kungiya Ta Faɗi Dalilin Tube Aminu Ado da Mayar da Sanusi II da Abba Ya Yi

legit.ng 2024/7/4
  • Wata kungiya a Arewacin Najeriya ta bankado cewa Gwamna Abba Kabir ya rushe masarautu ne domin kawar da hankulan mutane
  • Kungiyar ta zargi gwamnan da neman rufa-rufa kan gazawarsa a matsayin gwamna tsawon shekara daya da ya yi a mulki
  • Wannan na zuwa ne bayan tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero tare da mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kungiyar Arewa Truth and Justice Initiative ta yi martani kan rusa masarautun jihar Kano.

Kungiyar ta caccaki Abba Kabir kan tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero tare da mayar da Muhammadu Sanusi II.

Kwadinetan kungiyar, Kwamred Momoh Idoko shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Legit ta samu.

Momoh ya ce Abba Kabir ya yi hakan ne domin yin rufa-rufa kan gazawarsa game da mulkin jihar da ya yi a cikin shekara daya.

Har ila yau, kungiyar ta caccaki gwamnan kan rushe-rushe da ya yi yayin da ya yi fatali wurin inganta ilimi da tsaro da tattalin arziki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A kokarinsa na kawar da hankalin mutane kan gazawar da ya yi a mulki, Gwamna Abba Kabir ya bijiro da maganar rushe masarautu a jihar."
"Mun yabawa mutanen Kano saboda kin bari a yi wasa da hankalinsu wurin kin amincewa da tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero."

- Momoh Idoko

Karin bayani na tafe.....

Asali: Legit.ng

People are also reading