Home Back

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu, ya shiga fadar Masarautar Kano domin fara aiki.

dalafmkano.com 2024/6/26

Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, ya shiga fadar Masarautar Kano, a daren jiya Juma’a, domin fara aiki bayan da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bashi takardar kama aiki jiya a ɗakin taro na Afrika House da ke gidan gwamantin jihar.

Wata majiya ta shaidawa Dala FM Kano, cewa mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu, ya shiga masarautar ne a tsakar daren Juma’a, inda ya samu rakiyar Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da Kakakin majalisar dokokin jihar Hon. Jibril Isma’il Falgore, sauran ƴan tawagar gwamnan da Hakimai.

Idan dai ba’a manta ba a ranar Alhamis ne majalisar dokokin jihar Kano ta sanar da rushe sarakuna biyar da ke jihar, bayan da ƙudirin gaggawa kan gyaran dokar naɗa masarautun ta tsallake a zauren Majalisar, lamarin da daga bisani gwamna Abba Kabir, ya bayyana Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, a matsayin mai martaba sarkin Kano na 16.

Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar dokokin jihar Kano, kuma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala Lawan Hussaini Ciɗiyar Ƴan Gurasa, ne dai ya gabatar da ƙudirin gyara dokar masarautun, wanda yanzu haka tuni ta zama Doka, bayan da gwamnan Kano ya sa mata hannu.

Yanzu haka dai mai martaba sarkin Kano ya kwana a cikin fadar masarautar jihar, wanda zai fara aikin sa kamar yadda aka saba.

People are also reading