Home Back

Arsenal ta sayi mai tsaron raga David Raya

bbc.com 2024/8/25
A

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal ta dauki zaɓin sayan mai tsaron gidanta David Raya da tauka aro daga Brentford kan kudi fan miliyan 27.

Raya mai shekara 28 ya buga wasannin gasar Premier 16 ba tare da an zura masa kwallo a raga ba.

An zura masa kwallo 16 ne kacal a gasar Premier sannan a ƙarshe ya lashe kyautar maitsaron ragar da ya fi kowanne kokri a kakar da ta gabata.

Arsenal tana da mai tsaron ragarta Aaron Ramsadale, wanda ya buga mata wasanni 38 na kakar da aka yi ta 2022/23, ya buga wasanni 14 ba tare da an zura masa kwallo ba, kuma hakan ya sanya Mikel Arteta ya samu nutsuwa a zabin masu tsaron ragarsa.

A watan Agusta, dan wasan Spaniyan ya sanya hannu kan kwataragin shekara biyu da Bees kafin daga bisani ya koma Gunners a kakar a matsayin aro mai tsayi.

"Bayan shekara guda da na shafe a ƙungiyar a matsayin aro, yanzu dai zan iya cewa na zama cikakken dan wasan Arsenal nan da shekaru masu zuwa," in ji Raya.

"Ina cikin farin cikin jiran abin da zan iya gani a nan gaba, amma dole na yi murna da halin da ake ciki yanzu."

Arteta ya ƙara da cewa: Babban kamu ne da muka yi, zai ƙarawa tawagarmu kwarin gwiwa.

An sanya sunan Raya cikin tawagar Spaniya ta Euro 204, sai dai baya samun buga wasanni saboda Unai Simon babban mai tsaron ragar ƙasar.

People are also reading