Rikicin Sarauta: Kotu ta Haramtawa Gwamnatin Sokoto Tsige Hakimai
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Sokoto- Yayin da rikicin masarauta ke kara kamari a Sokoto, babbar kotun jiha ta dakatar da gwamna Ahmed Aliyu daga tsige hakimai biyu da ta dakatar a baya.
Hakiman na daga cikin masu rike da sarautu 15 da gwamnatin Sokoto ta dakatar daga kujerunsu a baya bisa wasu dalilinsu.
Punch News ta wallafa cewa hakiman Tambuwal, Buhari Tambuwal da na Kebbe, Abubakar Kassim ne su ka nemi kotu da dakatar da gwamnatin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari'a Kabiru Ibrahim Ahmed ya umarci gwamnatin jihar Sokoto da ta dakata da duk wani yunkurin tsige sarakuna.
Haka kuma kotun ta umarci fadar sarkin musulmi ta dakata da duk wani yunkuri da ta ke kokarin yi kan masarautun, Solace Base ta wallafa.
Gwamnatin jihar Sokoto dai ta yi yunkurin tsige wasu masu rike da sarautun gargajiya bisa zargin rashin biyayya.
A baya majalisar dokokin jihar ta kori masu rike da sarautar gargajiya 15, kuma sun samar da dokar da za ake ganin zai tsige sarkin musulmi.
Tuni lamarin ya yamutsa hazo har ta kai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya gargadi gwamnatin Sokoto kan yunkurin.
A wani labarin kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya gargadi gwamnatin jihar Sokoto kan tsige sarkin musulmi.
Kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ce ta yi ikirarin cewa akwai makarkashiyar tube rawanin Sarkin musulmin, Muhammad Sa'ad Abubakar III.
Asali: Legit.ng