Hajjin Bana: Kaduna Ta Yi Jigilar Alhazai Fiye Da 1,600 Zuwa Saudiyya
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta yi nasarar jigilar maniyyata fiye da 1,600 zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
Kashi na baya-bayan nan, wanda ya kunshi maniyyata 515, sun tashi ne a jiya Lahadi ta kamfanin Max Air, mai jigilar alhazan Kaduna.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Yunusa Muhammad ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
Ya ce, hakan ya kawo adadin maniyyata 1,612 da aka yi jigilarsu daga jihar ya zuwa yanzu.
Ya ce, a halin yanzu, an fara tantance maniyyatan da ake shirin jigila a jirgi na hudu a sansanin jigilar alhazai da ke Mando Kaduna, kuma a yau Litinin ne ake sa ran tashinsu.