Home Back

Ku dage da addu’o in samun zaman lafiya a ƙasa – Sarkin Kano

dalafmkano.com 2024/6/30

Mai martaba sarkin kano Malam Muhammadu Sunusi na biyu, ya yi kira ga al’ummar jihar nan da su ci gaba da addu’oin samun zaman lafiya mai dorewa a jihar kano da ma ƙasa baki daya.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da tsohon mataimakin gwamnan jihar kano Farfesa Hafizu Abubakar ya ziyarce shi yau a fadar sa, domin gaisuwa tare da yin mubaya’a ga mai martaba sarkin.

Sarkin Mallam Muhammadu Sunusi, ya kuma ce yana sane da irin gudunmuwar da Farfesa Hafizu Abubakar suke bayar wa wajen samun zaman lafiya da ci gaban jihar kano, inda ya kuma gode musu bisa wannan ziyara da suka kai masa fada.

A nasa jawabin tsohon mataimakin gwamnan jihar kano Farfesa Hafizu Abubakar, ya ce sun je fadar ne tare da rakiyar ɗan majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar gwale Abdulmajid Mai Rigar Fata, domin nuna goyon bayan su da kuma yin mubaya’a ga mai martaba sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi na biyu.

Haka zalika a zaman fadar na yau Laraba, mai martaba sarkin ya kuma karɓi baƙuncin shugaban hukumar Karota na jihar Kano Injiniya Faisal Muhmud, a fadar sa wanda yazo shima domin yin mubaya’a ga mai martaba sarkin.

Wakilin
mu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa, sarkin ya zauna a fadar sa domin karɓar gaisuwa daga al’ummar jihar Kano.

People are also reading