Home Back

Ana Tsaka da Rigimar Sarautar Kano, Kotu Ta Ɗauki Mataki a Shari'ar Tsige Ganduje

legit.ng 2024/10/5
  • Kotu ta ɗaga zaman sauraron shari'ar da aka nemi sauke Abdullahi Ganduje daga matsayin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa
  • Kungiyar ƴaƴan APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya ne suka kalubalanci Ganduje a kotu, sun ce naɗinsa ya saɓawa kundin mulkin jam'iyyar
  • Mai shari'a Inyang Ekwo ya ɗaga zaman zuwa ranar 5 ga watan Yuli domin bai wa masu kara damar martani kan ƙorafin Ganduje

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta sanya ranar 5 ga watan Yuli, 2024 domin fara sauraron ƙarar da aka nemi sauke shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje.

Mai shari'a Inyang Ekwo ta ɗauki wannan matakin ne domin bai wa masu kara damar martani kan ƙorafin da Ganduje ya shigar yana kalubalantar sahihancin ƙasar.

Abdullahi Ganduje.
Kotu za ta fara zaman shari'ar Ganduje da jiga-jigan APC na Arewa ta Tsakiya Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje Asali: Twitter

Wasu jiga-jigan jam'iyyar karƙashin kungiyar mambobin APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya ne suka maka Ganduje a kotu a ƙara mai lambaFHC/ABJ/CS/599/2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, masu kara karkashin Saleh Zazzaga sun tuhumi hanyar da aka bi wajen naɗa Ganduje a matsayin shugaban APC.

Masu ƙarar sun nemi kotu ta hana Ganduje ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar, cewar rahoton PM News.

Sun kuma roki kotun ta hana hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) amincewa da duk wani mataki da APC ta ɗauka karkashin Ganduje.

Masu shigar da kara sun shaida wa kotun cewa Ganduje ya ɗare kujerar shugaban jam’iyyar APC ne ba bisa ka’ida ba saboda ba dan shiyyar Arewa ta tsakiya ba ne.

Sun yi zargin cewa kwamitin zartaswa (NEC) na APC ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar lokacin ya ta nada Ganduje daga jihar Kano a shiyyar Arewa maso Yamma.

Budu da ƙari sun ce naɗa Ganduje ya maye gurbin Abdullahi Abdullahi ya saba wa doka ta 31.5 (1) f a kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC kuma NEC ta wuce gona da iri.

APC ta mayar da martani ga Atiku

A wani rahoton kuma APC mai mulki a Najeriya ba ta ji daɗin kalaman da Atiku Abubakar da jam'iyyarsa ta PDP suka yi ba kan Bola Ahmed Tinubu.

Jam'iyyar ta bayyana cewa ba daidai ba ne ɗora alhakin halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan kan Shugaba Tinubu.

Asali: Legit.ng

People are also reading