Home Back

Nazari Kan Yadda Ake Noman Albasa

leadership.ng 2024/5/18
Albasa

Mafi yawan lokuta, ana yin girbin Albasa ne a cikin watan Nuwamba zuwa watan Disamba, sannan kuma tana kai wa tsawon watannin uku zuwa hudu kafin ta kai ga kamala girma baki-daya.

A daukacin fadin duniya, an yi matukar amincewa da Albasa sakamakon irin muhimmancin da take da shi, musamman a wajen hada abinci mai kara inganta lafi da dadi tare kuma da wasu abubuwa da take da su na daban.

Idan za ka shuka Albasa a cikin fili, ka shuka Irinta ya kai kimanin santi mita biyu, zurfin kuma ya kasance kimanin inci daya. Idan kuma za ka shuka Irin ne a layi, an son kakar sararin da ya kai daga kimanin santi mita talatin zuwa sama.

A wadane Jihohi Aka Fi Noman Albasa A Nijeriya?
An fi yin noman Albasa a Jihohin Kano, Kaduna, Jigawa, Sokkwato, Filato, Bauchi da kuma Kebbi, inda a shekarar 2012 kadai aka samar da kimanin Albasa wanda yawanta ya kai tan 240,000 na danyarta, inda kuma aka samar da tan 1,350,000 shi ma na bushasshiyarta.

Zuwa Tsawon Wane Lokaci Albasa Ke Girma Bayan Shuka Ta A Nijeriya?
Sakamakon yanayin zangon lokacin noma ta; har zuwa lokacin da ake yin girbinta tare da kuma adana ta, yana da matukar kyau ga masu noman wannan Albasa su tabbatar da sun yi matukar kiyayewa wajen zabo Irin shukar ta da ya fi da cewa tare kuma da inganci.

Mafi akasari daga kashi biyar zuwa takwas na Albasar da ake nomawa, ana yi ne a kakar sanyi; domin tana iya jurewa kowane irin yanayi, har ila yau akasari ana shinfida gadon da za a reni Irin Albasar, wanda zai kasance ya kai fadin mita daya, sannan kuma fadin dai ya kasance iya girman Lambu ko gonar da za a shuka Albasar, inda ake bukatar kula da wajen renon har zuwa kwana arba’in kafin a cire a kai zuwa wani sabon gurin daban.

Bayan kammala dukkanin gyare-gyare, sai a sake zuba su a cikin kedojen da za a shukata ko a tukwane, sannan kuma kasar noman da za a shuka ta ta kasance marar karfi, musamman domin jijiyoyinta su kara habaka da kuma saurin girma.

Albasa ta fi bukatar kasar noman da ke dauke da sinadaran gargajiya ko kuma sinadaran da ake kira a turance ‘Alkaline Acidic da kuma phosphate’, har Ila yau, an fi so a sake mata matsuguni da yamma bayan an yi mata ban ruwa, kazalika kuma; ana yi mata canjin waje daga tsawon santi mita 5 ko kuma daga tsawon santi mita 7.5.

Haka zalika, yana da matukar kyau a rika cire mata ciyawa bayan duk sati biyu tare kuma da yi mata ban ruwa sau biyu a duk sati, musamman a lokacin kakar sanyi ana bukatar ka yi mata feshi da nau’in maganin feshi mai inganci.

Bugu da kari, ana bukatar manomin Dawa ya dinga zuba mata takin zamani na NPK bayan ya canza mata wajen da zai shuka ta, haka nan Albasa na fara nuna ne daga bayan kwana 84 zuwa kwana 100 bayan an canza mata waje, idan kuma za a yi mata girbi, ana yi ne ta hanyar yin amfani da hannu.

People are also reading