Home Back

Newcastle da West Ham sun yi cefane

bbc.com 2024/10/6

Asalin hoton, Getty Images

Sabbin 'yan wasan Premier League
Bayanan hoto, Newcastle ta ɗauki Lloyd Kelly (hagu), ita kuma West Ham ta sayo Luis Guilherme daga Palmeiras ta ƙasar Brazil

Mintuna 3 da suka wuce

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Newcastle ta sanar da ɗaukar Lloyd Kelly a kyauta.

Ɗan wasan bayan mai shekara 25 ya bar Bournemouth a ƙarshen kakar da aka kammala bayan kwantaraginsa ya ƙare a kulob ɗin.

Newcastle ta ce ɗan ƙwallon ya saka hannu kan yarjejeniya mai tsawo.

Sai dai Sky Sports ta fahimci cewa ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da kuma zaɓin tsawaita ta da shekara ɗaya.

Ita ma West Ham ta kammala ɗaukar Luis Guilherme daga kulob ɗin Palmeiras na ƙasar Brazil.

Matashin ɗan wasan mai shekara 18 ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da kulob ɗin na birnin Landan da ke buga gasar Premier League.

Ya buga wa babbar ƙungiyar Palmeiras wasa 40, inda har ya lashe babbar gasar ƙasar ta Brazilian Serie A.

Zai isa Landan ne bisa sharaɗin tantancewa da samun takardun biza da kuma na izinin aiki a Ingila.

People are also reading