Kallo ya Koma Sama: Sarkin Kano na 15 Aminu Bayero Zai yi Hawan Babbar Sallah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan masarautar Kano, sarki na 15, Aminu Ado Bayero zai yi hawan babbar sallah kamar sallah yadda aka saba a al'ada.
Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi a ranar Talata.
Daily Trust ta wallafa cewa sanarwar ta gayyaci dukkannin hakimai da sauran masu rike da sarauta su fito hawa tare da sarki Bayero.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta umarci dukkanin hakimai su fito da dagatan su da masu unguwanni da dawakai domin hawan sallah, kamar yadda Nigerian Tracker ta wallafa.
An kuma umarci hakiman da dagatai da su tabbata ba su makara ba domin karbar umarni daga sarki Aminu Bayero a ranar 9 Zul-hijjah 1445 A.H wanda ya yi daidai da 15 ga watan Yuni 2024.
Sanarwar ta kara da cewa tuni aka sanar da shugabannin kananan hukumomi shirye-shiryen hawan domin taimakawa da sufuri.
Sabon umarnin da sarki na 15 ya fitar ya zo ne bayan gwamnatin Kano ta tsige shi daga sarauta tare da nada Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon sarki.
A baya mun kawo mu ku labarin yadda 'yan sanda a Kano su ka kawo tsaiko kan shari'ar masarautar jihar tsakanin Aminu Bayero da Muhammadu Sanusi II a zaman kotu na yau.
'Yan sanda sun kawo tsaiko saboda rashin mika sammacin kotu ga wadanda ake kara a shari'ar da gwamnatin Kano ta shigar na hana Aminu Bayero ci gaba da zama a karagar mulki.
Asali: Legit.ng