Home Back

Kallo ya Koma Sama: Sarkin Kano na 15 Aminu Bayero Zai yi Hawan Babbar Sallah

legit.ng 2024/6/30
  • Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya fara shirye-shiryen gudanar da hawan sallah babba duk da dambarwar masarautar da har yanzu ke gaban kotu
  • A sanarwar da Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi ya sanyawa hannu, Sarkin Kano na 15 ya umarci hakimai su fiot da jama'arsu domin hawan sallah kamar yadda aka saba
  • Aminu Ado Bayero ya umarce su da su hallara a fadar sarki da ke Nassarawa da ranar 9 ga Zul-hijja, tare da gargadin ka da su makara domin karbar umarni na gaba kan batun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan masarautar Kano, sarki na 15, Aminu Ado Bayero zai yi hawan babbar sallah kamar sallah yadda aka saba a al'ada.

Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi a ranar Talata.

Aminu Ado Bayero
Sarkin Kano na 15 Aminu Bayero Zai yi hawan sallah Hoton: HRH ALH DR. AMINU ADO BAYERO CFR, EMIR OF KANO Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa sanarwar ta gayyaci dukkannin hakimai da sauran masu rike da sarauta su fito hawa tare da sarki Bayero.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kowa ya fito hawa," Sarkin dawakin Kano

Sanarwar ta umarci dukkanin hakimai su fito da dagatan su da masu unguwanni da dawakai domin hawan sallah, kamar yadda Nigerian Tracker ta wallafa.

An kuma umarci hakiman da dagatai da su tabbata ba su makara ba domin karbar umarni daga sarki Aminu Bayero a ranar 9 Zul-hijjah 1445 A.H wanda ya yi daidai da 15 ga watan Yuni 2024.

Sanarwar ta kara da cewa tuni aka sanar da shugabannin kananan hukumomi shirye-shiryen hawan domin taimakawa da sufuri.

Sabon umarnin da sarki na 15 ya fitar ya zo ne bayan gwamnatin Kano ta tsige shi daga sarauta tare da nada Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon sarki.

Shari'ar masarauta: 'Yan sanda sun kawo tsaiko

A baya mun kawo mu ku labarin yadda 'yan sanda a Kano su ka kawo tsaiko kan shari'ar masarautar jihar tsakanin Aminu Bayero da Muhammadu Sanusi II a zaman kotu na yau.

'Yan sanda sun kawo tsaiko saboda rashin mika sammacin kotu ga wadanda ake kara a shari'ar da gwamnatin Kano ta shigar na hana Aminu Bayero ci gaba da zama a karagar mulki.

Asali: Legit.ng

People are also reading