Home Back

Wace ce marigayiya Saratu Giɗaɗo wadda aka fi sani da Daso?

bbc.com 2024/5/3
..

Asalin hoton, Saratu Facebook

  • Marubuci, Usman Minjibir
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist

An haifi fitacciyar 'yar Kannywood, marigayiya Saratu Gidado da ake yi wa lakabi da Daso, a ranar 17 ga watan Janairu 1968, a birnin Kano.

Saratu Gidado ta yi makarantun firamare da sankandare a birnin Kano sannan kuma ta halarci kwalejin fasaha ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic, inda ta samu shaidar kammala babbar Diploma.

Jarumar ta shiga masana'antar fina-finan Kannywood ne a shekarar 2000, inda ta fara fitowa a wani fim mai suna Linzami da Wuta.

Kafin dai rasuwarta, jarumar ta sha tattaunawa da BBC, inda a ciki take bujuro da bayanai daban-daban da masu kaunarta ke son ji dangane da ita kuma za mu yi tsakure.

'Ina yin fim saboda mijina wayayye ne'

..

Asalin hoton, Daso Facebook

'Ina yin fim saboda mijina wayayye ne', kalamai ne da marigayiya Saratu Gidado ta yi yayin wata tattaunawa da ta yi da BBC Hausa a shekarar 2019.

"Mijina ya bar ni na ringa fitowa a fina-finan Hausa duk da ina da aure saboda mijina wayayye ne kuma mai ilimi. Sannan kuma a ina cikin harkar fim muka hadu da shi saboda haka bai hana ni ba.

Ya fahimci cewa ina da damar da zan yi aikin da nake so idan dai har zan kare mutumcina na 'ya Musulma kamar yadda duk wata mace ke aikin asibiti ko aikin jarida ko aikin koyarwa. Muna kiyaye mutumcin aurenmu da na iyalina" In ji Saratu.

Dangane kuma da yadda mai gidan nata yake ji a ransa idan ya ga tana wasan kwaikwayon, sai marigayiyar ta ce "ba ya jin komai tunda ya riga ya fahimci ba gaske ba ne. Ya san kwaikwayo ne. Ba ya jin komai."

'Ni ba muguwa ba ce kamar yadda nake fitowa a fim'

..

Asalin hoton, Daso Facebook

Marigayiya Saratu Gidado ta bayyana wa BBC cewa an fi ba ta damar taka rawa a zuwan 'muguwa', kasancewar ta iya taka rawar sosai.

"An fi ba ni damar taka rawar mai mugunta. Kuma mu mun san duk wani loko na mugunta amma fa a fim..hahahaha...Zan iya taka kowace irin rawa amma dai na fi jin dadin wannan din. Amma kowacce aka ba ni zan yi". In ji Daso.

To sai dai ta kara da cewa "amma fa a rayuwa ta hakika ba haka nake ba. Ni ba mamugunciya ba ce. Ni mai kirkir ce a zahiri. Karewa ma ni ba na magana sosai."

Bayan kwashekaru 18 a masana'antar fina-finan, sai marigayiyar ta yanke shawarar daina taka rawa ta fadace-fadace da guje-guje.

"yanzu gaskiya na koma taka rawar girma. Yanzu ba zan yi guje-gujen nan ba ko kuma na yi ta masifa saboda a kullum mutum girma yake yi.

'Babbar baiwar da Allah ya yi min'

A shirin BBC Hausa na ...Daga Bakin Mai Ita inda muke kawo jaruman fina-finan Kannywood, marigayiya Saratu Gidado ta shaida wa BBC cewa sirrinta da ba kowa ya sani ba a rayuwa shi ne "akwai baiwar da Allah ya yi min shi ne dan dai na yi wa mutum addu'a to insha Allahu kuwa za ta karbu."

To sai dai dangane da darasin da marigayiyar ta koya a rayuwa shi ne butulci.

"Darasi babba da na koya a wurin jama'a shi ne sai ka yi wa mutum halacci amma shi kuma ya yi maka butulci. Amma da ma ni don Allah nake yi wa mutane alkairi saboda haka idan ma sun yi butulcin to don kansu."

Wasu daga fina-finan da Daso ta yi

..

Asalin hoton, Daso Instagram

Kawo yanzu dai da wuya a iya hakkake yawan fina-finan da marigayiyar ta yi kasancewar ba ta raye ballanta ta tabbatar da hakan.

Sai dai kuma wasu fina-finan da suka fi yin fice nata sun hada da:

  • Nagari
  • Gidauniya
  • Mashi
  • Sarauniya
  • Daham
  • Alaqa
  • Fil'azal
  • Labarina
  • Sansani
  • Mazan fama
  • Gidan Iko
  • Cudanya
  • 'Yar Maiganye

Kafin rasuwarta kuma tana taka muhimmiyar rawa a wani fim mai dogon zango da bai fito ba tukunna mai suna Umarni.

Abin da 'yan Kannywood ke faɗa kan Daso

Tun bayan da Saratu Gidado ta rasu a ranar Talata, abokan aikinta a masana'antar ta Kannywood da sauran al'umma ke ta fadin irin kyawawan halayen maragayiyar.

ga kadan daga cikin wasu da BBC ta samu tattaunawa da su:

Abba Al-Mustapha - "Mun yi babban rashin jajirtacciyar tauraruwa. Allah ya gafarta mata.

Baballe Hayatu - "Babu abin da za mu ce sai Innalillahi wa Inna Ilaihirraji'un. Mun yi rashin baiwar Allah mai barkwanci. Allah ya gafarta mata."

Sahabi na kwana Casa'in - "Lallai wannan ba karamin rashi ba ne. Allah ya gafarta mata."

Alhassan Kwalli - " Ku san kamfanin na Sarauniya shi ne sillar janyo Daso cikin masana'anta. Muna zama lafiya. Mace ce mai son barkwanci. Muna fatan Allah ya karbi shahadarta."

Alaƙar Daso da BBC Hausa

Ku san za a iya cewa marigayiya Saratu Gidado na daya daga cikin 'yan Kannywood da ke da alakar mai karfi da sashen Hausa na BBC.

Ma'aikatan BBC Hausa sun hakkake cewa Daso ce mutum ta farko a mafi yawancin lokuta da ke fara bayyana ra'ayinta dangane da batutuwan da sashen ke wallafawa a shafukan sada zumunta.

Wani abu da ya banbanta marigayiya Saratu da sauran 'yan Kannywood shi ne a duk lokacin da BBC ta neme ta domin yin karin haske dangane da batutuwa to ba ta taba yin kasa a gwiwa ba.

A madadin shugaban sashen Hausa na BBC, malam Aliyu Tanko, daukacin ma'aikatan BBC Hausa na yi wa al'ummar Kano da na masana'antar Kannywood jajen rashin wannan fitacciyar jaruma.

People are also reading