Home Back

Gwamnan Kano ya kaddamar da bincike kan gwamnatin Ganduje

rfi.fr 2024/4/29

Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wasu kwamitoci biyu na alkalai domin gudanar da bincike barnatar da dukiyar al'ummar jihar da rikice-rikicen siyasa da bacewar wasu bayin-Allah a zamanin mulkin  Abdullahi Ganduje tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2023.

Wallafawa ranar: 04/04/2024 - 21:35

Minti 1

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf © Aminiya

Gwamna Yusuf ya bukaci mambobin kwamitocin da su yi aiki tukuru wajen zakulo duk wanda ke da hannu a ta'asar da aka tafka a lokacin mulkin na Ganduje.

Yusuf ya ce, gudanar da bincike kan barnatar da dukiyar talakawa na cikin alkawuran da ya dauka a yayin shan rantsuwar kama-aiki tare da zakulo da hukunta wadanda ke da hannu a rikice-rikicen siyasar da aka samu a jihar.

Rikicin siyasa shi ne babban kalubale ga dimokuradiyya a duk fadin duniya. Yana haddasa asarar rayuka da ta dukiya da kuma haifar da rashin yarda daga bangaren jama'a da masu mulki. Inji gwamnan na Kano.

Gwamnan ya dage kan cewa, lallai sai an binciki kashe-kashen da aka gani a shekarar 2023 domin hana sake aukuwar haka nan gaba.

Kwamitin farko karkashin mai shari'a Zuwaira Yusuf zai mayar da hankali kan rikice-rikicen siyasa da bacewar mutane da aka samu tsakanin 2015 zuwa 2023.

Sannan kwamiti na biyu karkashin mai shari'a Faruk Lawan, zai gudanar da bincike kan barnatar da dukiyar talakwan jihar ta Kano.

 
People are also reading