Home Back

Bayan Tsere Tsere da EFCC, Tsohon Gwamna a Arewa Zai Mika Kansa Gobe a Abuja

legit.ng 2024/7/4
  • A karbar, tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello zai gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya a gobe Alhamis a Abuja
  • Yahaya Bello ya samu tabbaci daga alkalin kotun cewa babu wani abu da zai same shi kan tuhumar da ake yi masa
  • Wannan na zuwa ne bayan tsere-tsere da tsohon gwamnan ya rinka yi da hukumar EFCC kan zargin wawushe kudin al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ana sa ran tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello zai gurfana a gaban kotu a gobe Alhamis 13 ga watan Yuni.

Bello zai kawo kansa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bayan tsere-tsere da hukumar EFCC kan zargin badakalar kuɗi.

Lauyan tsohon gwamnan, Abdulwahab Mohammed ya ce Bello ba ya tsoron EFCC amma yana tsoron halin da rayuwarsa za ta kasance a hannunsu a Abuja.

Muhammad ya ce ana yiwa Bello barazana a lokuta da dama a Abuja shiyasa ya ɓace gaba daya ba a ganinsa, cewar Leadership.

Ya ce tsohon gwamnan zai je kotu ne domin wanke kansa madadin ofishin hukumar EFCC a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Shari'a, Emeka Nwite ya ce hukumar EFCC tana bin doka kuma ba za ta yi wani abu da zai saɓa doka ba.

Ya ce Yahaya Bello ba shi kadai aka fara gayyata ba kan badakala kudi kuma ba zai zama na karshe ba.

EFCC ta shirya binciken El-Rufai

A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta zabi wasu daga cikin jami'anta domin fara binciken Nasiru El-Rufai.

Hukumar tana zargin tsohon gwamna da badakalar N423bn lokacin da ya ke mulkin jihar daga 2015 zuwa 2023.

Wannan na zuwa ne bayan Majalisar jihar Kaduna ta kafa kwamitin binciken El-Rufai kan wasu zarge-zarge.

Asali: Legit.ng

People are also reading