Home Back

Sin Ta Gabatar Da Takardar Shari’a Game Da Yadda Za A Yanka Wa Masu Neman Raba Yankin Taiwan Daga Kasar Sin Hukunci

leadership.ng 2024/7/7
Sin Ta Gabatar Da Takardar Shari’a Game Da Yadda Za A Yanka Wa Masu Neman Raba Yankin Taiwan Daga Kasar Sin Hukunci

Yau Jumma’a, kotun jama’a ta koli ta kasar Sin, da hukumar gabatar da kararraki ta koli ta kasar, da ma’aikatar tsaron jama’a, da ma’aikatar tsaron kasa, da ma’aikatar shari’a ta Sin cikin hadin gwiwa ne suka gabatar da takardar yanka hukunci ga masu neman raba yankin Taiwan daga kasar Sin bisa laifin raba kasa, da na rura wutar neman rabuwar kasa. Kana takardar za ta fara aiki a hukunce tun daga yau ranar 21 ga watan Yunin shekarar 2024.

Takardar ta nuna cewa, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su dauki alhakinsu da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, a kokarin kare mulkin kai, da ‘yancin kai, da cikakken yankunan kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

People are also reading