Home Back

MASIFAR TSADAR RAYUWA: Abincin da talakawa ke nomawa ya gagari talakawa dafawa su ci – Ƙididdigar NBS

premiumtimesng.com 6 days ago
GRAINS MARKET AT KAFIN MADAKI DISTRICT IN GANJUWA
GRAINS MARKET AT KAFIN MADAKI DISTRICT IN GANJUWA

Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa farashin tumatir, shinkafa da sauran kayan abincin da talakawa ke nomawa, ya yi tashin gwauron zabi a watan Mayu.

Daga cikin dalilan hauhawar farashin kayayyaki har da matsalar tsaro, wadda ta tilasta manoma ƙaurace wa gonakin su, saboda yawan garkuwa da su da ‘yan bindiga ke yi.

Tun ana yi wa manoma tsintar ɗai-ɗaya, har aka koma ana kwasar su da jidar su daga gonakin su, amma an kasa magance matsalar a Arewacin Najeriya.

Yayin da wake da shinkafa da tumatir da garin kwaki da masara suka ƙara tsada, NBS ta ce ba a taɓa ganin masifar tsadar kayan abinci kamar kwanan nan a ƙarshen Mayu zuwa shigar watan Yuni ba.

Cire tallafin fetur ya ƙara haukata farashin kayan abinci a Najeriya, saboda tsadar zirga-zirgar sufurin karakainar lodin kayan abinci zuwa kasuwanni, tsadar fetur domin sa wa janareto da kuma tsadar kayan noma.

Tuni dai talakawa suka ƙaurace wa wasu nau’ukan abincin da su kan su talakawan ke nomawa, amma kuma a yanzu ya gagare su.

Da yawa an koma cin wata shinkafa mai tsakuwa, wadda a talauce ake kira ‘afafata’, saboda rayuwa ta yi tsada.

A ƙarshen makon nan dai Gwamnatin Tarayya ta shawarci kowa ya yi azamar ɗaukar fartanya da garma, domin ya koma gona.

People are also reading