Gwamna Ya Fadi Yadda APC Za Ta Kwato Mulki a Jihar Edo Domin Samun Karin Jihohi Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Cross River - Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu ya ce APC ta daura damarar kwace wasu jihohin kudu maso kudu daga hannun jam'iyyun adawa.
Gwamnan ya fadi haka ne yayin da ake shirin fara zaben gwamna a jihar Edo a watanni ƙaɗan masu zuwa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamna Bassey Otu ya fadi haka ne yayin wani taron da jam'iyyar APC ta shirya a birnin Kalaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin taron jam'iyyar APC da ya gabata a Kalaba, gwamna Bassey Otu wanda shi ne kodinatan jam'iyyar APC a shiyyar kudu maso kudu ya ce jam'iyyar za ta kara kama jihohi a yankin.
Gwamna Bassey ya ce yana da karfin gwiwa a kan cewa za su kara samun nasara a jihohin kudu musamman a jihar Edo da ake kokarin yin zaɓe.
Bassey Otu ya ce shi kadai ne gwamnan a jam'iyyar APC a yankin kudu maso kudu kuma ya gaji da zaman kaɗaici saboda haka za su yi kokarin samun karin jihohi, rahoton Leadership.
Bayan haka shugaban kasa Bola Tinubu ma ya bayyana cewa akwai buƙatar samun karin jihohi a yankin domin samun albarkar da APC ke samarwa a ƙasa.
A watan Satumba mai zuwa ne za a yi zaben gwamna a jihar Edo kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar.
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa za ta yi dabarun da ta yi wajen samun nasara a jihar Imo domin kwace mulki a jihar Edo.
Gwamna Bassey Otu ya ce yana da tabbas kan cewa jihar Edo ba za ta kuɓuce musu ba saboda sun yi tanadi mai kyau domin tunkarar zaben.
A wani rahoton, kun ji cewa a lokacin da aka yi bikin ranar ma'aikata a Najeriya, gwamnan jihar Kuros Riba ya amince da sabon mafi karancin albashi.
Gwamna Bassey Otu ya amince da biyan N40,000 ga ma'aikatan jihar inda ya ce sun yi karin ne duba da halin da jihar ke ciki na kuncin rayuwa.
Asali: Legit.ng