Home Back

Rikicin Ƴan daba Yayi Sanadin mutuwar mutum 1, Da Raunata 2 A Kano

leadership.ng 2024/6/29
Rikicin Ƴan daba Yayi Sanadin mutuwar mutum 1, Da Raunata 2 A Kano

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a unguwar Ja-en Makera, inda suka kashe Muktar Garba tare da raunata wasu ‘yan sanda biyu.

Kwamishinan ‘yan sanda mai barin gado, AIG Usaini Gumel ne ya bayyana lamarin yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya ta wayar tarho a yau Alhamis.

Maharan ɗauke da muggan makamai, sun bijirewa jami’an ‘yan sanda tare da far wa mazauna unguwar. Garba, wanda aka fi sani da Babalia, ya rasu ne a asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda daga bisani aka mika gawarsa ga iyalansa domin yi masa jana’iza. Duk da kasancewar ‘yansanda wurin, ‘yan bindigar sun yi nasarar tserewa.

Ana ci gaba da kokarin ganowa tare da damke wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Gumel ya kuma tabbatar da wata arangama da ta shafi ‘yan daba a ƴan Dillalai da Ja-en Makera, wanda Ƴansanda suka tarwatsa.

‘Yansandan da suka samu  rauni sune; SC Wasilu Umar da PC Abdulmalik Yusif, sun samu kulawa likita kuma an sallame su.

An kama wani da ake zargi mai suna Umar Shuaibu da kai wa Yusif hari.

Tuni dai aka dawo da zaman lafiya, inda jami’an Ƴansanda ke ci gaba da sa ido.

People are also reading