Home Back

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Sin Da Turai Da Su Aiwatar Da Takara Mai Tsafta Don Cimma Nasara Tare

leadership.ng 2024/6/29
Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Sin Da Turai Da Su Aiwatar Da Takara Mai Tsafta Don Cimma Nasara Tare

Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ta gudanar da tarukan tattaunawa na kamfanonin Sin a Sifaniya, da Portugal, da Girka, da sauran wasu kasashen Turai, inda aka saurari muryoyi, da bukatun kamfanoni, da kungiyoyin kasuwanci na Sin dake kasashen Turai, kana bangaren Sin ya yi kira ga bangarorin Sin da na Turai da su warware takaddamar tattalin arziki, da cinikayya ta hanyar tattaunawa.

Kaza lika bangaren na Sin ya bukaci a kula da bukatun bangarorin biyu, don kaucewa habakar ricikin cinikayya. Kana Sin ta yi kira da a gudanar da hadin gwiwa don cimma nasara tare tsakanin bangarorin biyu, kuma ta yi maraba da gudanar da takara ta gari.

Yayin tarukan, wasu wakilan kamfanonin Sin sun bayyana cewa, a kwanan nan, kungiyar tarayyar Turai wato EU, ta ci gaba da yakar kamfanonin Sin, bisa hujjar wai “Yin Gasa Cikin Adalci”.

Bugu da kari, bisa binciken da kungiyar kasuwancin Sin ta EU ta yi, a shekaru hudu a jere, ra’ayin kamfanonin Sin game da yanayin kasuwanci a EU yana kara yin kasa, wanda ya dami mutane sosai.

Game da hakan, ministan kasuwancin Sin Wang Wentao, yayin da yake shugabantar taron masu ruwa da tsaki na kamfanonin Sin a birnin Lisbon fadar mulkin Portugal, ya bayyana cewa, zargin da wasu kasashe ke yi wa Sin na “Karancin adalci a takara”, ba shi da tushe ko kadan. Ya ce, takara ta adalci ita ce fahimtar juna tsakanin kasashen duniya, kuma ginshiki ce ta mu’amalar kasa da kasa, wadda ba za a bar wasu kasashe kalilan su yi iko da ita ba.

A zahiri, takara ta adalci, ya kamata ta kasance ta hanyar kokari, da himma domin cimma nasara, ba tare da neman hanyar takalar sauran sassa ba. Ya kamata ta kasance hanyar bude kofa da hadin gwiwa, da samun moriyar juna cikin daidaito, maimakon a rufe kai, da kebewa, ko hada wani gungu.

Kaza lika, ya kamata takara mai tsafta ta kasance ta bin ka’idojin da aka riga aka amince da su tsakanin kasa da kasa, maimakon a karya su, ko canza su bisa ra’ayin kashin kai. Sin tana maraba da hadin gwiwa da cimma nasara tare, amma ba ta tsoron takara, kana tana maraba da takara ta gari, tare da adawa da takara mai nufin hana ci gaba. (Safiyah Ma)

People are also reading