Home Back

Amurka ta ce bata samu takardar neman ficewar sojojinta a Nijar ba tukuna

rfi.fr 2024/5/7
Wasu sojoji a sanssanin dakarun Amurka da ke Jamhuriyar Nijar kenan.
Wasu sojoji a sanssanin dakarun Amurka da ke Jamhuriyar Nijar kenan. © AFP

Wani babban jami’in ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ya ce, har yanzu gwamnatin kasar bata samu wata takarda ta musamman daga gwamnatin mulkin Nijar na neman ficewar dakarunta daga kasar ba, yana mai cewa ta samu alamu daban-daban da ke nuna cewa ba a maraba da kasancewar daruruwan sojojin Amurka a can.

Celeste Wallander, mataimakin sakataren tsaro kan harkokin tsaro na kasa da kasa, ya shaidawa kwamitin kula da harkokin tsaro na majalisar dokokin kasar cewa, kawo yanzu majalisar mulkin sojan Nijar ba ta nemi sojojin Amurka da su fice daga kasar ba a hukumance.

Amurka dai na da dakaru kusan 650 da kuma wasu daruruwan da ke aikin wanzar da zaman lafiya har yanzu a Nijar, wadda a baya ta kasance cibiyar yaki da ta'addanci.

Wallander ya ce Amurka na ci gaba da duba hanyoyin da za a bi wajen gudanar da ayyukan yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a yankin.

“A Jamhuriyar Nijar, ma'aikatan Amurka sun hada karfi da karfe wajen amfani da jiragen yaki masu saukar ungulu domin kawo karshen ayyukan masu tayar da kayar baya,” in ji mataimakin sakatariyar yada labaran Pentagon, Sabrina Singh.

Sauye-sauyen dangantakar tsakanin kasashen biyu, ya sa wasu 'yan majalisar dokokin Amurka nuna shakku kan yadda Nijar za ta iya janyewa daga wani shirin kawance aikin soja cikin kankanin lokaci.

Shugaban Rundunar Sojojin Amurka a Afirka, Janar Michael Langley, ya ce rashin fahimtar juna ya taka rawar gani sosai a Nijar da ma gwamnatoci da dama da ke yankin Sahel a shekarun baya-bayan nan.

Langley ya ce ya nemi ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ba da karin kayan aiki don dakile tasirin kasar Rasha a wannan kasa da ma sauran kasashen yankin Sahel.

People are also reading