Home Back

Amincewar Shugaban Kasa Kawai Muke Jira Mu Yi Kidaya A Nuwamba – NPC

leadership.ng 2024/8/23
Amincewar Shugaban Kasa Kawai Muke Jira Mu Yi Kidaya A Nuwamba – NPC

Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta ce ta shirya tsaf domin gudanar da sabon ki-dayar jama’a da gidaje a watan Nuwamban 2024.

Da yake ganawa da ‘yan jarida kan bikin tunawa da ranar kidaya ta duniya ta ba-na, shugaban hukumar, Nasir Isa Kwarra, ya ce, yunkurin nasu na kan zaman ji-ran amincewar Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu domin gudanarwa.

Kwarra ya shaida cewar hukumar ta kammala shirye-shiryenta zuwa kaso 70 na gudanar da kidayar, ya ce, rashin gudanar da kidayar a kan lokaci ba zai hana kasar nan cimma zagayen Majalisar Dinkin Duniya na 2020, kan kidayar mutane da gidaje ba.

Idan za a tuna dai, Nijeriya ba ta gudanar da aikin kidaya ba tsawon shekaru 18 da suka gabata, inda aka yi yunkurin gudanarwa a shekarar 2023, inda daga bisani tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya soke tare da hannanta da-mar hakan ga sabuwar gwamnatin da za ta gajeshi.

“Muna son gudanar da aikin kidaya a Nuwamba, amma muna jiran sahalewar shugaban kasa. Idan mun samu damar hakan, nan da nan za mu gudanar da ki-dayar a shekarar 2024, kuma za mu gudanar da nagartacce kuma karbabben ki-daya a Nijeriya.

“Muna kan shirye-shiryenmu. An kashe kudade sosai. Tun da kidayace ta zamani ce, muna da sama da 760,000 PDAs da za su taimaka mana wajen aikin kidayar. Wannan kayan aikin mun sayo sama da shekara. Irin wadannan kayan idan ba a yi amfani da su ba, baturansu za su mutu, muna fargabar yin asararsu. Yana da kyau a sani muna da kayayyakin aikin gudanar da kidayar.”

Ya kara da cewa hukumar tana da taswirar zamani na gudanar da kidaya, kuma idan an kammala kidayar za a bai wa kowa wani dan kasa damar da yake bukata da samun bayanansa cikin sauki.

A nasa bangaren, babban jami’in kiddiga na kasa, Adeyemi Adeniran, ya ce, ta hanyar tattara bayanai da aka samu daga kidaya za a iya samun hanya mafi sauki na magance matsalolin da suke tattare da farara da talauci.

People are also reading