Home Back

"Ku Mayar da Ni Jiha Ta": Yahaya Bello Ya Nemi Alfarma Daya Wajen EFCC, Ya Jero Dalilai

legit.ng 2024/7/4
  • Yayin da ake ci gaba da tuhumar Yahaya Bello kan badakala, ya nemi alfarma guda daya wajen hukumar EFCC a Abuja
  • Tsohon gwamnan Kogi ya ce bai kamata a ci gaba da tuhumarsa a Abuja ba tun da ba a can ya aikata abin da ake zarginsa ba
  • Ya roki hukumar EFCC da ta dawo da shi jihar Kogi domin ci gaba da tuhumar da ake yi masa madadin tsare a birnin Abuja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nemi alfarma wajen hukumar yaki da cin hanci ta EFCC.

Yahaya Bello ya roki hukumar da ta dawo da shi jihar kogi domin ci gaba da tuhumarsa a can

Gwamnan ya bayyana haka ne ganin cewa a jihar ya aikata abin da ake zarginsa a kai, kamar yadda TVC News ta ruwaito

Ya ce ya fi dacewa a ci gaba da rike shi a jihar Kogi inda ake zarginsa madadin tsare shi a birnin Abuja.

Hakan ya biyo bayan zargin badakalar N80bn da ake yiwa tsohon gwamnan lokacin da yake mulkin jihar, cewar Daily Post.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigob PDP ya gano maboyar Yahaya Bello

A wani labarin, kun ji cewa babban jigon jam'iyyar PDP, Austin Okai, ya fallasa wurin da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ɓuya don kaucewa kamen EFCC.

Mista Okai ya bayyana cewa yanzu haka Yahaya Bello na cikin gidan gwamnatin Kogi da ke Lokoja ya ɓuya.

Tun a watan Afrilun da ya gabata hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta ayyana neman tsohon gwamnan ruwa a jallokan zargin badakalar N80bn.

Asali: Legit.ng

People are also reading